An yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a mahaifar sa

An yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a mahaifar sa

- A daren jiya ne aka yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a mahaifarsa, garin Hadejia, dake jihar Jigawa

- Ya rasu a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu a kasar Jamus yana da shekaru 73 a duniya bayan kamuwa da rshin lafiya

- AVM Hamza Abdullahi (mai ritaya) ya taba zama gwamnan jihar Kano a mulkin soji sannan ya taba rike mukamin minista

A daren jiya, Juma'a, ne aka yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a mahaifar sa, garin Hadejia, dake jihar Jigwa.

Manyan 'yan siyasa, shugabannni masu ci da tsofi, malamai da sarakuna sun halarci jana'izar da aka yi a daren na ranar juma'a.

Hamza Abdullahi, tsohon gwamnan jihar Kano kuma tsohon ministan gwamnatin tarayya, ya rasu a kasar Jamus.

Tsohon babban jami’in sojan mai ritaya yayi aiki a matsayin gwamnan jihar Kano a mulkin soja daga 1984 zuwa 1985, lokacin shugaban kasa Muhammadu Buhari na a matsayin shugaba a mulkin soja.

An yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a mahaifar sa

An yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a mahaifar sa
Source: Facebook

An yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a mahaifar sa

An yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a garin Hadejia
Source: Facebook

An yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a mahaifar sa

An yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a mahaifar sa
Source: Facebook

An yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a mahaifar sa

An yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a Hadejia
Source: Facebook

An yi jana'izar marigayi AVM Hamza Abdullahi a mahaifar sa

Ganduje da Sule Lamido a wurin jana'izar
Source: Facebook

Tsohon ministan ya rasu a kasar Jamus a ranar Laraba, 2 ga watan Janairu, wasu majiyoyi suka tabbatar da hakan ga TheCable. Ya rasu yana da shekaru 73 a duniya bayan kamuwa da rashin lafiya.

DUBA WANNAN: Rundunar soji ta kama mutane 71 a jihar Adamawa

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci sallar jana'izar marigayin akwai tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sarkin Dutse, Nuhu Sanusi da sauran su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel