Masu garkuwa da Mutane 4 sun shiga hannu a jihar Legas

Masu garkuwa da Mutane 4 sun shiga hannu a jihar Legas

Ba bu shakku dangane yadda lamarin tsaro ke ci gaba da dagulewa a kasar nan ba bu dare ba bu rana, ta'addanci musamman garkuwa da mutane ya yi kamari wajen addabar al'umma cikin wasu jihohi a Kudu da Arewacin Najeriya.

A yayin haka, cikin wani rahoto da muka samu da sanadin shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, wasu miyagun 'yan ta'adda masu garkuwa da mutane sun shiga hannun tsaro ta 'yan sanda a jihar Legas da ke Kudancin kasar nan.

'Yan ta'addan hudu sun shiga hannu biyo bayan samun nasara gami da tsayuwa bisa aiki ta hukumar 'yan sanda reshen leken asiri bisa jagorancin kungiyar sufeto janar na 'yan sanda, Ibrahim K. Idris.

Daya daga cikin 'yan ta'adda da ya shiga hannu a kwana-kwanan nan, Sani Muhammad, ya shaidawa jami'an tsaro cewa, wannan azal ta shiga hannun hukuma ta haramta masu samun Naira miliyan 500 na kudaden fansar garkuwa da mutane a garin Abuja da kuma Kaduna da suka nufaci samu a watan Dasumba kadai.

Masu garkuwa da Mutane 4 sun shiga hannu a jihar Legas

Masu garkuwa da Mutane 4 sun shiga hannu a jihar Legas
Source: UGC

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, 'dan ta'addan ya shiga hannu tare da tawagarsa ta Mutane uku a jihar Enugu inda suke cin karen su ba bu babbaka wajen addabar al'umma.

Shigar 'yan ta'addan hannun jami'an tsaro ta biyo bayan wani tuggu da suka kulla na garkuwa da wani hamshakin dan kasuwa mazanin garin Abuja, Alhaji Ulere.

Sauran 'yan ta'addan da suka hannu tare da Sani sun hadar da Babangida Garba, Dogo Ibrahim, da kuma Ibrahim Haruna. Sun shaidawa aniyyarsu ta samun dukiya ta kimanin Naira miliyan 500 na kudin fansa da suka nufaci karbewa hannun wadanda suka kudiri yin garkuwa da su a watan Dasumba.

KARANTA KUMA: Dole Buhari ya sha kasa a zaben 2019 - Jerry Gana

Sani wanda ya kasance dan asalin jihar Zamfara ya shaidawa jami'an tsaro cewa, ya yi fice wajen ta'addancin fashi da makami da kuma garkuwa da mutane da ya fara shekaru biyu da suka gabata bayan da neman duniya ya rufe masa idanu.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Legas, Moshood Jimoh, ya tabbatar da wannan lamari da cewa, 'yan ta'addan sun shiga hannu tare da makaman su yayin da suka cin karen su ba bu babbaka a kan hanyar Enugu zuwa birnin Fatakwal.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, Dakarun sojin Najeriya, sun samu nasarar ragargazar wasu 'yan ta'adda da suka saba addabar al'umma a yankunan karamar Tsafe ta jihar Zamfara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Mailfire view pixel