Manyan Labarai A Yau
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya fito ya yi martani kan sukar da Alhaji Atiku Abubakar ya yi wa gwamnatinsa. Ya ce kowa yana yin kuskure.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya bayyana kalar yarjejeniyar da za a kulla da Iran. Trump ya bayyana cewa za ta fi wadda aka kulla a baya kyau.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi magana kan yaki da Iran. Trump ya musanta cewa Isra'ila ce ta sanya ya fara yaki kasar Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Jam'iyyar ADC mai adawa ta yi magana kan batun cewa tana shirin hadewa da PRP. Ta bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a batun kawancen da ake yadawa.
Dakarun IRGC na kasar Iran sun sanar da sake rufe mashigar Hormuz bayan takaddama da Amurka. Hakan ya sa an kawar da hasashen raguwar farashin fetur a Najeriya.
'Yan bindiga dauke da makamai sun kai sababbin hare-haren ta'addanci a jihar Plateau. 'Yan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC daga PDP. Shekarau ya taba sauya sheka zuwa jam'iyyun a baya.
Magoya bayan tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da na Peter Obi sun kafa sabuwar kungiyar siyasa domin tunkarar babban zaben shekarar 2027.
Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya yi ta'aziyyar rasuwar So Fada na masarautar Bida karkashin Etsu Nupe. Ya ce marigayi ya taka rawa wajen kawo cigaba.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari