Dama Ta Samu: Davido Zai Raba Jarin Kasuwanci ga 'Yan Najeriya
- Davido ya ce gidauniyarsa za ta samar da jarin fara kasuwanci ga ’yan Najeriya masu dabarun sana’a domin taimaka musu su fara gudanar da ayyukansu
- Mawakin ya bayyana cewa shirin na cikin abubuwan da zai gudanar yayin bikin cikarsa shekara 34 a ranar 21 ga Nuwamba
- Ya ce shirin zai fara ranar Litinin, amma bai bayyana adadin kuɗin tallafin ko sharuddan zaɓen waɗanda za su amfana ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Fitaccen mawakin Afrobeats, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya sanar da shirin samar da jarin fara kasuwanci ga ’yan Najeriya masu dabarun sana’a a matsayin wani ɓangare na bikin cikarsa shekara 34.
Mawakin zai cika shekara 34 a ranar 21 ga Nuwamba, kuma ya ce gidauniyarsa za ta tallafa wa masu burin fara kasuwanci a bana. Davido ya shahara ba kawai a fannin waƙa ba, har ma da ayyukan jin ƙai da taimakon al’umma.

Source: Facebook
Yadda Davido zai taimaki masu son fara sana’a
A cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Juma’a, 20 ga watan Nuwamban 2026 mawakin ya bayyana cewa gidauniyarsa za ta faɗaɗa tallafin da ta saba bayarwa a lokacin bikin zagayowar ranar haihuwarsa.
Ya ce baya ga aika kuɗi ga gidajen marayu kamar yadda ta saba yi a baya, gidauniyar za ta tallafa wa ’yan Najeriya masu ra’ayoyin kasuwanci da ke buƙatar jari domin fara sana’arsu.
Davido ya ce an ƙaddamar da shirin ne domin taimaka wa ’yan Najeriya da ke fuskantar matsin tattalin arziki su samu damar kafa sana’o’insu.
"A bana, a bikin ranar haihuwata, gidauniyata ba za ta aika kuɗi ga gidajen marayu kawai kamar yadda muka saba ba, za mu kuma taimaka wa ’yan Najeriya masu ra’ayoyin kasuwanci da jarin fara sana’a, saboda mun san irin wahalar da ake ciki a ƙasar.” In ji shi.

Kara karanta wannan
APC ta bayyana gaskiyar da ta yarda da ita kan matsalar rashin tsaro a gwamnatin Tinubu
Ba a bayyana adadin tallafin ba
Ana sa ran shirin zai samar da tallafin kuɗi ga ’yan Najeriya masu dabarun kasuwanci waɗanda ba su da isasshen jari domin aiwatar da manufofinsu.
Sai dai mawakin bai bayyana adadin kuɗin da gidauniyarsa za ta ware domin shirin ba.
Haka kuma, bai bayyana sharuddan da za a bi wajen zaɓen waɗanda za su amfana da tallafin ba.
Ya kuma ce shirin zai fara aiki ne a ranar Litinin, 23 ga watan Nuwamban 2026 amma bai yi ƙarin bayani kan yadda masu sha’awar neman tallafin za su aika da bayanan dabarun kasuwancinsu ba.
A cikin saƙonsa, Davido ya ce: “Za mu fara ranar Litinin.”
Shirin ya ƙara yawan ayyukan jin ƙansa
Wannan sabon shiri ya ƙara cikin ayyukan jin ƙai da Davido ya gudanar a baya, inda ya riƙa tallafa wa ƙungiyoyin agaji da kuma mutanen da ke buƙatar taimako.
A wannan karon, mawakin ya faɗaɗa tallafin da yake bayarwa ta hanyar mayar da hankali kan taimaka wa masu son kafa sana’o’i, musamman a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tattalin arziki.

Source: Facebook
Gwamnatin Edo ta soki Davido
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Edo ta bukaci fitaccen mawakin Afrobeat, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, da ya mayar da hankali wajen yin wakokin da za su taimaka masa ya lashe kyautar Grammy.
Gwamnatin ta bukaci Davido ya mayar da hankalin ne maimakon barazanar neman Shugaban Amurka Donald Trump ya sa baki kan zaben gwamnan jihar Osun.
Asali: Legit.ng

