Yadda Amurka da Israila Suka Kashe Yara Sama da 600 a Iran
- Mataimakiyar shugaban ƙasar Iran mai kula da harkokin mata da iyali, Zahra Behrouz-Azar, ta ce yara 623 sun mutu a yaƙin Amurka da Isra’ila
- Ta ce wasu yaran da suka tsira sun samu munanan raunuka, ciki har da yanke gaɓoɓin jiki, karaya da ƙonewa mai tsanani
- Iran ta ce ta shigar da ƙara a kotunan Amurka da wasu ƙasashen Turai kan harin makarantar Minab da kisan Ayatollah Ali Khamenei
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Tehran, Iran - Gwamnatin Iran ta bayyana cewa yara sama da 600 sun mutu sakamakon yaƙin da Amurka da Isra’ila suka ƙaddamar kan ƙasar, yayin da wasu da dama suka samu munanan raunuka.
Mataimakiyar shugaban ƙasar mai kula da harkokin mata da iyali, Zahra Behrouz-Azar, ta ce adadin yaran da suka mutu ya kai 623.

Source: Getty Images
Yara 623 sun mutu a yaƙin Amurka da Isra’ila
Ta bayyana hakan ne yayin wani taro da aka shirya domin karrama waɗanda suka rasa rayukansu a yaƙin, cewar rahoton tashar Aljazeera.
A cewarta, waɗanda suka mutu sun haɗa da ɗaliban makarantu biyu da ke birnin Minab, a kudancin Iran.
Kamfanin dillancin labaran Iran, IRNA, ya ruwaito ta tana cewa abin da ya faru da yaran ya kasance babban abin takaici da baƙin ciki.
Wasu yaran da suka tsira sun samu munanan raunuka
Behrouz-Azar ta ce yaran da suka tsira daga hare-haren sun fuskanci raunuka masu tsanani waɗanda za su iya sauya rayuwarsu har abada.
Raunukan sun haɗa da yanke wasu gaɓoɓin jiki, karayar ƙasusuwa da kuma ƙonewa mai tsanani.
Ta jaddada cewa wajibi ne a fito fili a yi magana kan irin waɗannan raunuka da kuma matsalolin da yaran ke fuskanta sakamakon yaƙin.
A cewarta, wahalar da yaran da suka samu raunuka ke ciki ba ta samun kulawar da ta dace, duk da munin abin da suka fuskanta.
Iran ta ce ta shigar da ƙara a kotunan Amurka da Turai
A wani labarin makamancin haka, gwamnatin Iran ta ce ta shigar da ƙara a kotunan Amurka da wasu ƙasashen Turai kan harin da aka kai makaranta a Minab, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Ta kuma ce ƙorafin ya shafi kisan jagoran addini kuma shugaban ƙasar na lokacin, Ayatollah Ali Khamenei.
Mataimakin shugaban Iran mai kula da harkokin shari’a, Majid Ansari, ya ce an fara shari’o’in ne a kotunan da suka amince suna da hurumin sauraron waɗannan ƙorafe-ƙorafe.
Kamfanin dillancin labaran IRNA ya ruwaito Ansari yana cewa ana gudanar da shari’o’in ne bisa hujjoji da takardun da aka tattara.
Ya bayyana cewa an riga an shigar da wasu ƙorafe-ƙorafen, yayin da ake ci gaba da shirya wasu domin yin rajistar su a kotuna.

Source: UGC
Iran ta kakkabo jirgin yakin Amurka
A wani labarin kuma, kun ji cewa Iran ta yi ikirarin kakkabo jirgin leken asirin Amurka kirar MQ-9 a sararin samaniyar mashigar ruwan Hormuz.
Iran ta bayyana cewa Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) ta ce rundunar tsaron sararin samaniyarta ce ta yi amfani da sabon tsarin kariyar sama wajen gano jirgin da kuma kakkabo shi.
Asali: Legit.ng

