Sojoji Sun Goge Rubutun da Suka Yi bayan Ganin Ministan Tsaro a Kamfen Tinubu

Sojoji Sun Goge Rubutun da Suka Yi bayan Ganin Ministan Tsaro a Kamfen Tinubu

  • Ma’aikatar Tsaro ta Najeriya ta cire wani saƙo da ta wallafa a kafofin sadarwa game da gangamin yaƙin neman zaɓen APC mai mulki
  • Wasu ’yan Najeriya sun zargi Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, da amfani da muƙaminsa wajen shiga harkokin siyasa
  • Saƙon ya jawo martani daga masu amfani da kafafen sada zumunta, inda wasu suka tambayi dalilin halartar ministan taron siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ma’aikatar Tsaro ta Najeriya ta goge wani saƙo da ta wallafa game da gangamin yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu.

Rundunar ta goge rubutun ne da aka gano ministan tsaro, Christopher Musa a kamfen jam’iyyar APC mai mulki, bayan ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin ’yan Najeriya.

Rundunar tsaro ta goge rubutu kan kamfen Tinubu
Ministan tsaro, Christopher Musa sanya da hular APC a wurin kamfen. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Source: Facebook

Sakon da rundunar ta wallafa

A cikin saƙon da ma’aikatar ta wallafa, ta bayyana cewa Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, ya gudanar da rangadin duba wurin da za a gudanar da gangamin a daren Juma’a, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya je Maiduguri, ya fito da abubuwa 3 da za su sa 'yan Arewa su nemi canji a 2027

Saƙon ya ce:

“Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, OFR, ya gudanar da binciken gani da ido a wurin da za a gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a jihar a daren Juma’a, a matsayin wani ɓangare na shirye-shiryen dabarun tsaro gabanin taron. A yayin ziyarar, Janar Musa ya zagaya wurin.”

Sai dai wasu ’yan Najeriya sun yi amfani da kafafen sada zumunta wajen zargin ministan da cin zarafin muƙaminsa ta hanyar shiga harkokin siyasa.

Tinubu ya dauki alkawari kan wutar lantarki
Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Najeriya. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

Alawarin da Tinubu ya dauka

Shugaba Bola Tinubu da wasu manyan jiga-jigan APC sun halarci gangamin a ranar Asabar, inda shugaban ƙasar ya nemi goyon bayan jama’a ga jam’iyyar tare da yin alƙawarin inganta samar da wutar lantarki da sauran abubuwa.

A yayin jawabinsa, Tinubu ya ce za a samu sauyi mai kyau a bangaren wutar lantarki.

“Za ku gani, kuma ina tabbatar muku cewa za a samu ingantuwar wutar lantarki. Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, yana aiki tuƙuru tare da tawagarsa,” in ji shugaban ƙasar.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a jihar Kano ya yi ƙamari, an aika saƙon gaggawa ga Tinubu da Abdulaziz Yari

Ya ƙara da cewa:

“Kun zaɓi APC da gagarumin rinjaye a zaɓen da ya gabata. Dole ne ku ci gaba da kasancewa tare da mu. Dole ne. Saboda ci gaba, wadata da bunƙasar ƙasarmu, da kuma makomar ’ya’yanku da jikokinku.”

Kafin ma’aikatar ta goge saƙon nata daga shafin X, ya riga ya jawo martani daga masu amfani da kafar, cewar Tribune.

Wasu sun nuna damuwa kan kasancewar Ministan Tsaro a irin waɗannan tarukan siyasa, musamman a daidai lokacin da Najeriya ke fuskantar ƙalubalen tsaro da suka haɗa da ayyukan ’yan bindiga.

Wani mai amfani da X mai suna Nnamdi Agbo Junior, wanda aka fi sani da Atabor Jagaban, ya rubuta cewa:

“Sanye da hular APC? Wannan cin zarafin muƙami ne, don Allah!”

Rundunar tsaro ta tona asiri kan ta'addanci

Mun ba ku labarin cewa Rundunar tsaro ta ce makiyayan waje ne ke kai hari a jihohin Benue da Plateau, sun Najeriya ta iyakoki masu rauni.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Yan ta'adda sun kai hari kan tawagar Sanata Monguno da wasu jiga jigan APC

Sojoji sun kama fitattun masu garkuwa da mutane da dillalan makamai, ciki har da wani 'dan ta'adda mai suna Nkwachi Eze.

An ji cewa an ceto mutane 173 da aka sace, an kama masu laifi 430, an kuma dakile satar man da ya kai sama da N1.9bn.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.