Baturiya Ta Zargi Sarkin Daura Ta Ci Mata Zarafi a Fadarsa

Baturiya Ta Zargi Sarkin Daura Ta Ci Mata Zarafi a Fadarsa

  • Wata mata da ke amfani da sunan ‘beduina’ a intanet ta zargi Sarkin Daura da taɓa ƙirjinta ba tare da izininta ba yayin ziyarar fadarsa
  • Matar ta ce lamarin ya faru ne ranar 14 ga Nuwamba, 2026, bayan ta yi tafiyar kwanaki 30 a sassa daban-daban na Najeriya
  • Zargin ya jawo muhawara sosai, yayin da Majalisar Masarautar Daura da gwamnatin Katsina ba su fitar da sanarwar martani ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Sarkin Daura, Faruk Umar Faruk, ya shiga muhawara a kafar sada zumunta ta X bayan wata matafiya ’yar ƙasar waje ta zarge shi da taɓa jikinta ba bisa ƙa’ida ba yayin ziyarar da ta kai fadarsa a jihar Katsina.

Zargin ya biyo bayan yaɗuwar wani bidiyo a kafafen sada zumunta, wanda ya nuna yadda basaraken ke tattaunawa da matar yayin ziyarar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gamu da gagarumar matsala a cikin APC kan shirinsa na tazarce a 2027

An yi zargi kan Sarkin Daura
Mai martaba Sarkin Daura, Umar Farouk Bashir Hoto: Masarautar Daura
Source: Facebook

Baturiya ta zargi Sarkin Daura da cin zarafinta

Matar, wadda ke amfani da sunan ‘beduina’ a intanet, ta bayyana zargin ne a wani saƙon da ta wallafa a shafinta na Instagram bayan kammala rangadin kwanaki 30 a sassa daban-daban na Najeriya.

Ta ce lamarin ya faru ne ranar Asabar, 14 ga Nuwamba, lokacin da ta ziyarci fadar Sarkin Daura.

Yadda matar ta ce lamarin ya faru

A cikin bayaninta, matar ta ce an kai ta wani ɗaki mai kyau a cikin fada, inda ta zauna tare da basaraken suka fara tattaunawa.

Ta yi zargin cewa Sarkin ya riƙe hannunta, yana wasa da shi, kafin ya rungume ta tare da sumbatar kumatunta.

Sai dai ta ce abin ya ɗauki wani yanayi mai tayar da hankali lokacin da basaraken ya taɓa ƙirjinta, kamar yadda ta bayyana a saƙonta.

“Hakan ya ba ni mamaki sosai. Na ce masa, ‘Sarki, a’a, a’a, a’a, a’a. Sarki, ba za ka riƙa taɓa ni haka ba’, amma sai ya ci gaba da dariya.” In ji ta.

Kara karanta wannan

Dama ta samu: Davido zai raba jarin kasuwanci ga 'yan Najeriya

Matar ta bayyana cewa abin da ya fi ba ta mamaki shi ne yadda lamarin ya faru a cikin fada, duk da cewa ta yi tafiya a sassa daban-daban na Najeriya ba tare da fuskantar irin wannan cin zarafi a wuraren taruwar jama’a ba.

Ta ce ba a taɓa cin zarafinta ta fuskar lalata ba a lokacin da take tafiya a titunan Najeriya, har ma a wuraren da jama’a suka cika.

Sai dai ta ce ta yi mamakin fuskantar irin wannan yanayi a fadar wani basarake da ya kamata ya kasance abin koyi wajen ɗabi’a da mutunci.

Matar ta ce har yanzu tana tunawa da abin da ya faru

Matar ta bayyana abin da ta ce ya faru a matsayin abin ƙyama, tana mai cewa har yanzu tana yawan tuna lamarin.

Ta ce zargin ya faru mako guda kafin ta fito fili ta bayyana shi, amma ta jira sai da ta bar Najeriya kafin ta yi magana a kai.

Ta kuma yi zargin cewa mai yiwuwa ba ita ce mace ta farko da basaraken ya yi wa irin wannan abu ba, duk da cewa ba ta gabatar da wata hujja da ke tabbatar da zargin ba.

Kara karanta wannan

An ba 'yar Amurka Dala miliyan 4.5 bayan ta yi hira da Shugaba Tinubu? Gaskiya ta bayyana

Matar ta ce tana zargin cewa watakila ita ce mace ta farko da ta samu damar adana hujjar abin da ta ce ya faru.

A cewarta, tana amfani da tabarau masu ɗaukar bidiyo na kamfanin Meta, kuma ta kunna su cikin gaggawa lokacin da lamarin ya faru.

Zargin ya jawo martani a kafafen sada zumunta

Bayan wallafa zargin, mutane da dama sun yi martani a kafar X, inda wasu suka nuna damuwa tare da buƙatar a ɗauki matakin da ya dace kan lamarin.

Sai dai ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Majalisar Masarautar Daura da gwamnatin jihar Katsina ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan zargin ba.

An zargi Sarkin Daura
Baturiyar da ta yi zargi kan Sarkin Daura Hoto: Beduina
Source: Instagram

Sarkin Daura na goyon bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sarkin Daura da ke jihar Katsina, Alhaji Umar Farouq-Umar, ya bayyana dalilin goyon bayan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Alhaji Umar Farouq-Umar ya ce yana goyon bayan Tinubu ne saboda girmama masarautar Daura da jihar Katsina ta hanyar yi wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari jana’izar da ta dace da matsayin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng