NDC a Kano Ta Fitar da Kwamitin Kamfen, Ta Saka Sunan Shugaban NNPP a Ciki
- Jam’iyyar NDC a Kano ta naɗa shugaban NNPP na jihar, Hashimu Sulaiman Dungurawa, a kwamitin yaƙin neman zaɓenta
- An sanar da naɗin Dungurawa ne cikin jerin sunayen mambobin kwamitin gudanar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na jam’iyyar a Kano
- Sauran waɗanda aka naɗa sun haɗa da Shehu Wada Sagagi a matsayin darakta janar, yayin da Sunusi Usman Dambatta zai zama mataimakinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) a Kano ta naɗa shugaban jam’iyyar NNPP a cikin kwamitin kamfen dinta.
NDC ta saka Hashimu Sulaiman Dungurawa, a matsayin babban kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓenta gabanin babban zaɓen 2027.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Dungurawa ya ci gaba da riƙe shugabancin NNPP, jam’iyyar da aka fi sani da tambarin littafi, tun bayan sauya sheƙar Rabiu Musa Kwankwaso da magoya bayansa zuwa NDC.
An bayyana naɗin Dungurawa ne cikin jerin sunayen mambobin kwamitin gudanar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da na gwamna na jam’iyyar a Kano.
Da aka tuntube shi domin tabbatar da labarin naɗin nasa, Dungurawa ya amince cewa an naɗa shi, inda ya bayyana matakin a matsayin falala daga Allah.
Ya ce:
“Wannan falala ce daga Allah."
Jerin sunayen ya kuma nuna cewa an naɗa Hon. Shehu Wada Sagagi a matsayin Darakta Janar na kwamitin yaƙin neman zaɓen, yayin da Hon. Injiniya Sunusi Usman Dambatta zai zama mataimakinsa.
Sauran naɗe-naɗen sun haɗa da Hon. Danlami Zakari Unguwar Gettai, wanda zai zama mataimakin darakta janar mai kula da Kano ta Arewa, da Hon. Bello Aliyu Kiru, wanda zai kula da Kano ta Kudu.
Haka kuma, an naɗa Hon. Dakta Sale Adamu Kwaru a matsayin mataimakin darakta janar mai kula da Kano ta Tsakiya.
A gefe guda, Hon. Adamu Aliyu Kibiya ne zai zama sakataren yaƙin neman zaɓen, yayin da aka naɗa Hon. Ibrahim Garba a matsayin mataimakin kakakin kwamitin.
Karin bayani na tafe....
Asali: Legit.ng
