"Tinubu Ya Gaza": An Kwadaitar da 'Yan Najeriya Amfanin Zaben Peter Obi a 2027

"Tinubu Ya Gaza": An Kwadaitar da 'Yan Najeriya Amfanin Zaben Peter Obi a 2027

  • Moses Cleopas ya ce Peter Obi, ɗan takarar NDC a zaɓen 2027, ne kaɗai zai iya taimakawa wajen farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya
  • Shugaban NDC ya buƙaci ’yan Najeriya su yi amfani da zaɓensu wajen sauya gwamnatin Shugaba Bola Tinubu saboda matsalolin tattalin arziki da tsaro
  • Cleopas ya ce ya kamata a tantance ’yan takara bisa tarihinsu, ƙwarewarsu da dabarun magance matsalolin ƙasa, ba addini ko biyayya ga jam’iyya ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) na ƙasa, Moses Cleopas, ya bayyana ɗan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027, Peter Obi, a matsayin fatan Najeriya na farfaɗo da tattalin arziki da sake gina ƙasar.

Cleopas ya bayyana hakan ne ranar Juma’ar da ta gabata yayin bikin cikarsa shekara 57 a duniya, wanda aka gudanar a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

"Tinubu bai fi ya lashe jihohi 2 ba"; An yi sabon hasashe kan zaben shugaban kasa

An bukaci a zabi Peter Obi a 2027
Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Osa Director, mai magana da yawun NDC na ƙasa, ya fitar, cewar rahoton jaridar TheCable.

Tsohon sanatan ya yi kira ga ’yan Najeriya da su sauke nauyin da ke kansu na ƙasa ta hanyar kada ƙuri’unsu domin sauya Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.

Ya zargi gwamnatin Tinubu da gaza aiwatar da manufofin da za su inganta rayuwar ’yan ƙasa, musamman a wannan lokaci da ake fama da matsin tattalin arziki.

Cleopas ya soki gwamnatin Tinubu

Shugaban NDC ya ce Najeriya ba za ta iya sake shafe wasu shekaru huɗu a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu ba, yana mai cewa gwamnati ta gaza magance matsalolin tattalin arziki, rashin tsaro da kuma tsadar rayuwa.

Ya bayyana cewa zaɓen 2027 ya kamata ya zama kamar ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a kan yadda gwamnatin Tinubu ta gudanar da mulki.

A cewarsa, bai kamata shugaban ƙasa ya samu wa’adin mulki na biyu saboda goyon bayan siyasa kawai ba, sai dai bisa la’akari da irin ayyukan da ya gudanar a wa’adin farko.

Kara karanta wannan

Shettima ya kwantar da hankalin Igbo, ya yi masu albishir kan kujerar shugaban kasa

“Zaɓen wa’adin mulki na biyu kamar ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ne. Ana tantance mutum ne bisa ayyukan da ya yi a baya. Idan ya yi abin kirki, sai a sake ba shi dama. Idan kuma bai yi abin da ya kamata ba, sai a nemi ya koma gida.” In ji shi.

Ya bukaci a tantance ’yan takara bisa ƙwarewa

Cleopas ya shawarci ’yan Najeriya da su tantance ’yan takarar shugaban ƙasa bisa irin tarihin ayyukansu, ƙwarewarsu da kuma yadda za su iya fahimtar matsalolin ƙasar tare da samar da hanyoyin magance su.

Ya jaddada cewa bai kamata mutane su zaɓi shugabanni saboda addini ko biyayya ga wata jam’iyya kawai ba.

A nasa ra’ayin, ya kamata a mayar da hankali kan irin gudummawar da ’yan takara za su iya bayarwa wajen magance matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

Shugabanni sun yaba wa Cleopas

Mambobin Majalisar Dokokin Jihar Bayelsa, ’yan jam’iyyar NDC da shugabannin addinai da suka halarci bikin sun bayyana Cleopas a matsayin shugaba mai hangen nesa, wanda ya himmatu wajen hidimar jama’a da kyakkyawan shugabanci.

A nasa ɓangaren, Osa Director ya yaba wa shugaban jam’iyyar bisa hikima, dattako da kuma ƙwarewarsa a harkokin siyasa.

Ya ƙara da cewa Cleopas ya taimaka wajen bunƙasa NDC har ta zama ɗaya daga cikin manyan jam’iyyun adawa masu saurin yaɗuwa a Afirka, wadda mutane da dama ke nuna sha’awa a kanta.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya zayyano matsalolin dan takarar na ADC a 2027

Peter Obi na neman shugabancin Najeriya a 2027
Dan takarar shugaban kasa na NDC, Peter Obi na jawabi a wajen taro Hoto: Mr. Peter Obi
Source: Facebook

Shettima ya kwatanta farin jinin Buhari da Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Kashim Shettima, ya ce ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ba zai kai farin jinin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba.

Shettima ya bayyana hakan a jihar Anambra, yayin da yake jagorantar gangamin yaƙin neman zaɓe domin neman wa’adin mulki na biyu ga Shugaba Bola Tinubu. Re

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng