Shettima Ya Kwantar da Hankalin 'Yan Igbo, Ya Yi Masu Albishir kan Kujerar Shugaban Kasa

Shettima Ya Kwantar da Hankalin 'Yan Igbo, Ya Yi Masu Albishir kan Kujerar Shugaban Kasa

  • Kashim Shettima ya yi hasashen cewa yankim Kudu maso Gabashin Najeriya zai samar da shugaban ƙasa a nan
  • Shettima ya bayyana hakan ne a gangamin APC a Awka, inda ya bukaci ’yan Kudu maso Gabas su rungumi haɗin kan ƙasa da kyautata alaƙa da sauran yankuna
  • Ya bayyana cewa nasarar zaɓe a Najeriya na buƙatar ƙulla kawance tsakanin yankuna, inda ya yi amfani da tarihin marigayi Muhammadu Buhari a matsayin misali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Anambra - Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa yankin Kudu maso Gabashin Najeriya ne zai samar da shugaban ƙasa idan mulki ya koma Kudu bayan kammala wa’adin mulkin Shugaba Bola Tinubu.

Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 19 ga watan Nuwamban 2026 yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Awka, babban birnin jihar Anambra.

Shettima ya ba 'yan Igbo shawara
Kashim Shettima a wajen taron APC a Anambra Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

A yayin jawabinsa, ya bukaci al’ummar Igbo su rungumi haɗin kan ƙasa, juriya a harkokin siyasa da kuma ƙarfafa alaƙarsu da sauran yankunan Najeriya, cewar rahoton jaridar TheCable.

Shettima ya yi magana kan shugabancin ƙasa

Mataimakin shugaban ƙasar ya ce yana da tabbacin cewa idan mulki ya koma yankin Kudu a wa’adin mulkin da zai biyo bayan na Tinubu, yankin Gabashin Najeriya ne zai samu damar samar da shugaban ƙasa.

“A wa’adin mulkin da zai biyo baya, idan mulki ya koma Kudu, ina tabbatar muku cewa mulki zai samu matsuguninsa a yankin Gabas.” In ji shi.

Ya kuma bayyana Shugaba Tinubu a matsayin abokin al’ummar Igbo, inda ya yi nuni da alaƙar iyalinsa da yankin Kudu maso Gabas a matsayin hujjar yadda gwamnatinsa take kallon yankin.

Ya magantu kan alaƙar Tinubu da Igbo

“Shugaba Tinubu abokin Ndigbo ne. Ɗansa, Seyi, ya auri wata mata ’yar asalin Igbo. Da a ce yana ƙin al’ummar Igbo, da bai amince ɗansa ya auri mace ’yar Igbo ba. Saboda haka, mu al’umma ɗaya ne.” In ji shi.

Mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana al’ummar Igbo a matsayin muhimmin ɓangare na siyasa da tattalin arzikin Najeriya.

Ya yi iƙirarin cewa kusan ’yan Igbo miliyan 17 ne ke zaune a Arewacin Najeriya, yayin da wasu miliyan 10 ke zaune a Legas kaɗai.

Wace shawara Shettima ya ba 'yan Igbo?

Shettima ya shawarci al’ummar Igbo da kada su bari bambancin ra’ayin siyasa ko ra’ayin ƙabilanci ya lalata alaƙarsu da sauran ’yan Najeriya.

Ya bukace su da su riƙa tuntuɓar sauran al’umma da ƙulla kawance a sassa daban-daban na ƙasar domin ƙarfafa haɗin kai.

A matsayin misali, ya yi amfani da tarihin siyasar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, inda ya ce samun nasarar zaɓe a Najeriya na buƙatar haɗin kai da goyon baya daga wajen yankin da ɗan takara ya fi samun karɓuwa.

Shettima ya ce Buhari ya tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓuka uku daban-daban, amma bai samu nasara ba, duk da cewa yana da ƙaƙƙarfan tushen goyon baya a Arewacin Najeriya.

Shettima ya je kamfen Anambra
Kashim Shettima tare da Gwamna Chukwuma Soludo a wajen kamfen din APC a Anambra Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Sule Lamido ya ba Shettima shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sule Lamido ya shawarci Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima da ya riƙa taka-tsantsan wajen furta kalamansa a bainar jama’a.

Sule Lamido ya buƙaci Shettima ya nuna natsuwa, sanin ya kamata da kuma girman da ake buƙata daga mutumin da ke riƙe da babban muƙami a ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng