Tsohon na Kusa da Atiku Ya Zayyano Matsalolin dan Takarar na ADC a 2027
- Segun Sowunmi ya ce ’yan Najeriya sun sha ƙin zaɓen Atiku Abubakar a zaɓukan shugaban ƙasa da ya tsaya takara
- Tsohon kakakin kamfen ɗin Atiku ya tambayi dalilin da ya sa matasan Arewa za su ci gaba da mara masa baya
- Sowunmi ya ce har yanzu ba a tabbatar da takarar Atiku a ƙarƙashin ADC ba, duk da ɗaukaka ƙarar da jam’iyyar ta yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani jigon jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya soki yawan yunƙurin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na neman shugabancin Najeriya.
Sowunmi ya yi ikirarin cewa ’yan Najeriya sun sha ƙin amincewa da burin Atiku na zama shugaban ƙasa a lokutan zaɓe daban-daban.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2026 yayin wata tattaunawa da ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels TV.

Kara karanta wannan
Sabon tsarin da Kwankwaso yake so a yi amfani da shi a zaben shugaban kasa a Najeriya
Sowunmi, wanda kuma mamba ne a kwamitin kamfen ɗin APC, ya yi wannan tsokaci ne yayin da ake tambayarsa game da ra’ayin Atiku na cewa shi ya fi Shugaba Bola Tinubu cancantar jagorantar Najeriya.
Ya tambayi dalilin ci gaba da takara
Da yake mayar da martani, Sowunmi ya ce ya kamata tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya sake nazarin burinsa na ci gaba da neman shugabancin Najeriya.
“To, ya daɗe yana faɗin haka, amma ’yan Najeriya sun sha ƙin amincewa da shi.” In ji shi
Ya kuma tambayi dalilin da zai sa matasan Arewa masu ƙwazo da ƙwarewa su ci gaba da zagayawa tare da Atiku a duk lokacin da ya nemi takara.
A kalamansa:
“Idan ka yi zaɓe sau da dama kamar yadda Waziri (Atiku) ya yi, akwai wani abu da ya kamata shi kansa ya yi tunani a kai. Yaushe yake tsammanin matasan Arewa masu ƙwazo da basira za su gaji da ci gaba da tafiya tare da shi?”

Kara karanta wannan
Peter Obi ya shirya share hawayen 'yan Arewa, ya gano hanyar magance matsalar yankin
Batun wanda zai fito daga Arewa
Sowunmi, wanda ya taɓa zama kakakin ƙungiyar kamfen ɗin Atiku Abubakar a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, ya kuma yi tambayoyi kan dabarun siyasar tsohon mataimakin shugaban ƙasar.
Ya ce Arewa ta riga ta samu damar samar da shugaban ƙasa wanda ya yi shekara takwas a kan mulki, wato tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya kuma yi tambaya kan sahihancin takarar Atiku a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, bayan hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ya soke shugabancin kwamitin riƙon ƙwarya da tsohon shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, ke jagoranta.
Sowunmi ya ce takarar Atiku ba ta tabbata ba
Sowunmi ya dage cewa har yanzu ba a tabbatar da Atiku a matsayin ɗan takarar ADC ba, duk da cewa jam’iyyar ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotun.
"Ya zuwa yau, ba ya cikin waɗanda za su fito a takardar zaɓe. Shin saboda ka ɗaukaka ƙarar shari’ar da ka faɗi a ƙaramar kotu, hakan yana nufin za ka ci nasara ne? Abin da ya fi muhimmanci shi ne, ya zuwa yau, ba shi ne ɗan takararsu ba.” In ji shi.
Ya kuma zargi Atiku da rashin tafiyar da rikicin da ya shafi Nafiu Bala Gombe yadda ya kamata, inda ya bayyana salon mu’amalarsa da kalmar “emir complex”, wato ɗabi’ar wanda yake ganin kansa a matsayin sarki.
"Sarakuna ba sa roƙo, ba sa zuwa ziyartar mutane ko kiran wasu. Suna zama a gida ne, kowa ya zo wajensu. Eh, za ka iya zama sarki, amma ba za ka iya zama sarki ba idan kana neman tikitin takara a jam’iyyar wani mutum.” In ji shi.

Source: Facebook
Yadda Atiku ke ji kan Tinubu Must Go
A wani labarin kuma, kun ji cewa Atiku Abubakar ya bayyana yadda yake ji a duk lokacin da magoya bayansa ke yi wa Shugaba Bola Tinubu ihun ‘Tinubu Must Go’ a wajen gangamin siyasa.
Ya ce duk lokacin da ya ji jama'a suna ihun 'Tinubu Must Go' a gangaminsa, yana ɗaukar kalaman a matsayin kira na neman sauyin shugabanci da kuma tunatarwa kan nauyin da zai hau kansa idan aka ba shi amanar mulki.
Asali: Legit.ng
