'Tinubu na Fuskantar Barazanar Rasa Kuri'u Sama da Miliyan 3 a 2027'

'Tinubu na Fuskantar Barazanar Rasa Kuri'u Sama da Miliyan 3 a 2027'

  • Wata kungiyar APC Rescue Movement ta yi gargadin cewa Bola Tinubu na iya rasa kuri'u sama da miliyan uku a zaben 2027 saboda rikicin cikin gida
  • Kungiyar ta ce jihohi 13 zuwa 17 na fama da rikice-rikicen siyasa, yayin da sama da 'yan takara 1,000 da magoya baya ke nuna rashin jin dadi
  • Ta bukaci Tinubu da shugabannin APC su gaggauta sulhunta masu korafi, tare da tabbatar da adalci, gaskiya da hada kan mambobin jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wata kungiyar hadakar jiga-jigan jam'iyyar APC ta yi gargadin cewa rikice-rikicen cikin gida na iya jawo wa Shugaba Bola Tinubu asarar kuri'u sama da miliyan uku a babban zaben 2027.

Kungiyar mai suna APC Rescue Movement ta bayyana cewa rashin gamsuwar wasu 'yan takara, wadanda suka kafa jam'iyyar da magoya bayanta na iya kawo cikas ga burin Tinubu na sake lashe zaben shugaban kasa.

Kara karanta wannan

'Asirina zai tuno': Gwamna ya ce zai shiga matsala idan Tinubu ya faɗi zaɓe

Kungiya ta yi gargadi kan rikicin APC
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

A wata sanarwa da mai kula da kungiyar na kasa, Abdullahi Aliyu Katsina, ya fitar a Abuja, kungiyar ta ce jihohi tsakanin 13 zuwa 17 na fuskantar rikice-rikicen cikin gida da ka iya raunana tsarin jam'iyyar, cewar Punch.

Ta danganta matsalar da rashin fahimtar juna tsakanin shugabanni, ware wasu wadanda suka kafa APC da kuma rashin tuntubar masu ruwa da tsaki da suka taimaka wajen kafa jam'iyyar da samun nasarorinta a zabuka.

Binciken da ƙungiyar ta gudanar

Kungiyar ta ce bincikenta ya gano sama da 'yan takarar siyasa 1,000 da ke cikin fushi, wadanda suka kafa jam'iyyar sama da 100,000 da kuma kusan magoya baya miliyan 2.8 da korafe-korafensu ke shafar amincinsu ga APC.

Sai dai ta jaddada cewa wadannan alkaluma ba kuri'un da jam'iyyar ta riga ta rasa ba ne, illa kuri'un da za ta iya rasa idan ba a dauki matakan gyara ba.

Ta ce har yanzu akwai damar magance matsalar ta hanyar sulhu na gaskiya, adalci da bai wa kowane bangare damar shiga harkokin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Disamba ta karato: Gwamna ya ware N50,000 ga kowane ma'aikaci a jiharsa

Kungiyar ta nuna damuwa kan yadda APC ke mayar da hankali kan tarukan siyasa da tallata 'yan takara, maimakon warware matsalolin da ke damun mambobinta.

Ta ce nasarar siyasa ba ta dogara da gangamin yakin neman zabe, fastoci da goyon bayan manyan mutane kadai ba, domin amincewar magoya baya da jajircewarsu na da muhimmanci.

An gargadi Tinubu kan rikicin APC
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Gargadin da kungiyar ta yi

Haka kuma, kungiyar ta yi gargadi kan tasirin matsin tattalin arzikin da 'yan Najeriya ke fuskanta tare da karuwar rashin gamsuwa a cikin jam'iyyar mai mulki.

Ta yi nuni da taken siyasa mai suna BA MA YI, wanda ta ce yana samun karbuwa a wasu tarukan yakin neman zabe a sassan kasar.

A cewarta, bai kamata shugabannin APC su dauki wannan batu a matsayin korafin yau da kullum ba, domin yana iya zama alamar rashin jin dadin wasu al'ummomi da masu ruwa da tsaki.

Kungiyar ta bukaci Tinubu, shugaban APC na kasa, mambobin kwamitin gudanarwa na kasa (NWC), gwamnonin jam'iyyar da sauran masu ruwa da tsaki su fifita sulhu da adalci kan bukatun kansu.

Kungiyar ta tabo batun N30bn da walwalar ma'aikata

Kara karanta wannan

'Na samu tabbaci': Tinubu ya ce zai je ya yi barci bayan abin da ya gani a Kebbi

Baya ga rikicin siyasa, kungiyar ta nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da kudaden APC, tana mai bukatar karin bayani game da zargin saka sama da Naira biliyan 30 a wani tsarin jari na kwanaki 90.

Ta ce tattaunawar da ta yi da shugaban ma'aikatan shugaban APC na kasa ta sa ta dakatar da matsayarta na daukar matakin shari'a kan lamarin na wani lokaci domin samun karin bayani.

Kungiyar ta kuma bukaci shugabannin APC su yi bayani dalla-dalla kan yadda aka gudanar da jarin da kuma yadda zai taimaka wajen samar wa jam'iyyar 'yancin cin gashin kanta na kudi.

A bangaren walwalar ma'aikata kuwa, ta bukaci a inganta yanayin aikin ma'aikatan sakatariyar jam'iyyar ta kasa, musamman batun aiwatar da mafi karancin albashi tsakanin Naira 70,000 da Naira 100,000.

Tinubu ya gamu da matsala

An ji cewa kungiyar APC Northern Youths Forum ta ce ba za ta sake tallatawa ko yaƙin neman zaɓen mai girma Shugaba Bola Tinubu ba.

Ƙungiyar ta danganta matsayinta da matsalar tsaro, tsadar rayuwa da kuma zargin cewa gwamnatin Tinubu ta yi watsi da yankin Arewa.

Shugaban ƙungiyar ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna son kai wajen rabon mukamai, yana mai cewa ta fifita na kusa da madafun iko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.