Manyan Labarai A Yau
An yada wani rahoto mai cewa gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya karbe iko da kudaden kananan hukumomi. Kungiyar ALGON ta fito ta yi jawabi kan zargin.
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima, ya yi gargadin cewa akwai sauran aiki wajen yaki da ta'addanci duk da nasarorin da aka samu.
Wani malamin addinin Kirista a kasar Ghana, ya yi hasashen nasarar Peter Obi a zaben shekarar 2027. Ya ba shi shawarar abubuwan da ya kamata ya yi.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta tsayar da Abba Kabir Yusuf a matsayin dan takararta na gwamnan jihar Kano a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta tabbatar da Gwamna Nasir Idris a matsayin dan takararta na gwamna a jihar Kebbi a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Babbar kotun tarayya mai zama a Abuja ya aoke jadawalin zaben fitar da gwani, mika sunayen yan takara da maye gurbin wasu da INEC ta kakaba wa jam'iyyun siyasa.
Jam'iyyar APC ta tabbatar da Gwamna Dauda Lawal a matsayin 'dan takarar gwamnan jihar Zanfara a zaben 2027, ya samu tikitin tazarce ba tare da hamayya ba.
'Yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da mataimakiyar shugaban karamar hukuma a jihar Ekiti. Daga baya jami'an tsaro sun samu nasarar ceto ta.
Hukumar kula da Alhazai ta kasa (NAHCON) ta kammala aikin jigilar maniyyata zuwa kasa mai tsarki. An fara shirye-shiryen dawo da su gida Najeriya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari