Manyan Labarai A Yau
Babbar hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana nasarorin da aka samu kawo yanzu a hadin gwiwar sojojin kasar nan da na Amurka, yak ta'adda 175 sun tafi lahira.
Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya gana da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Peter Obi ya gana da Kwankwaso ne a gidansa da ke Abuja.
Wannan na zuwa ne yayin da kwamitin ADC ke ci gaba da aikin tantance masu neman takarar shugaban kasa, inda Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana domin cika sharadi.
Mai magana da yawun gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya zargi madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da yi wa Tinubu aiki.
Hadimin tsohon mataimakin shugaban kasa, Paul Ibe ya tabbatar da cewa babu wasa a batun neman taiarar shugaban kasa na Atiku Abubakar a jam'iyyar ADC
Gwamnatin jihar Kano ta sanar da rufe makarantu a fadin jihar. Gwamnatin ta bayar da hutun ne domin babbar sallah. Ta bayyana ranakun da za a koma.
Janar Theophilus Danjuma ya bayar da N3bn yayin kaddamar da littafin tarihin Yakubu Gowon a Abuja, yayin da Aliko Dangote ya sayi kwamitin littatafan a kan N500m.
Jam'iyyar NDC ta bayyana sunayen mutanen da ta saka a kwamitik tantance masu neman takarar shugaban kasa, gwamnoni, da yan Majalisar tarayya da jihohi.
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya bayyana Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II a matsayin aboki na kwarai, lamarin da ya ba mutane dariya a taro.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari