Ciyaman Ya Yi Martani ga Amnesty game da Kalaman Barazana da Ya Yi kan Zaɓen APC

Ciyaman Ya Yi Martani ga Amnesty game da Kalaman Barazana da Ya Yi kan Zaɓen APC

  • Shugaban karamar hukumar Gwale a Kano, Abubakar Ma’azu Mojo, ya kalubalanci kungiyar Amnesty International
  • Mojo ya ce kungiyar ta yi watsi da ayyukan alherin da ya gudanar a Gwale, inda ya ce ya taimaka wajen dakile daba, dawo da yara makaranta
  • Ya kuma jaddada cewa ba ya fada da kowa, yana mai cewa zai ci gaba da goyon bayan gwamnatin Abba Kabir Yusuf da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano – Shugaban karamar hukumar Gwale, Abubakar Ma’azu Mojo, ya mayar da martani ga kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty.

Hakan ya biyo bayan ta soki kalaman da ya yi kan yadda jam’iyyar APC za ta gudanar da zaɓen 2027.

Ciyaman ya sha suka game da kalamansa
Gwamna Abba Kabir Yusuf da shugaban karamar hukumar Gwale, Abubakar Ma’azu Mojo. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Abduljabar Mahmoud Aisami.
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar Amnesty International ta nuna damuwa kan kalaman shugaban karamar hukumar, inda ta bayyana cewa irin wannan furuci na iya haddasa tashin hankali a lokacin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Hadarin jirgin ruwan da aka yi a Najeriya ya shafi kamfen din APC na 2027

Lamarin ya samo asali ne bayan wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta, wanda aka ga Mojo yana kira ga magoya bayan APC da su tabbatar da samun nasarar jam’iyyar ta kowace hanya.

A yayin wani taro da magoya bayan APC, shugaban karamar hukumar ya bukace su da su shirya tsaf domin fafatawar siyasa mai zafi, tare da tabbatar da cewa jam’iyyar ta lashe zaɓe a rumfunan da suke.

Ya yi amfani da kalaman cewa dole ne su tabbatar da nasarar APC a rumfunan zaɓensu, ko da kuwa ta hanyar amfani da duk wata dabara.

A martanin da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mojo ya zargi Amnesty International da ɗaukar wani ɓangare na kalamansa tare da yin watsi da sauran ayyukan da ya ce ya gudanar domin ci gaban al’ummar Gwale.

Ya bayyana sukar da kungiyar ta yi masa a matsayin abin dariya, inda ya kwatanta lamarin da wani karin magana na Hausawa game da yaron da ya tsinci haƙori.

Mojo ya ce ba sa gaba da kowa, yana mai bayyana gamsuwarsa da shugabancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da sauran ‘yan takarar APC gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Ciyaman a Kano ya ballo ruwa, ya yi barazana ga jama'a kan zaben APC a 2027

A cikin martaninsa, ya ce:

“Na ji cewa Amnesty International na kira da a kama ni. Don Allah, su mayar da ni ƙwallon ƙuli-ƙuli. Idan sun kama ni, su kulle ni sannan su jefa ni cikin teku. Idan sun ga dama, su sake ni bayan zaɓe ko kuma su ci gaba da tsare ni.
“Ina Amnesty lokacin da na dakile ayyukan daba? Ina suke lokacin da na mayar da yara 501 makaranta? Da dama daga cikin waɗannan matasa sun kammala karatu da sakamako mai kyau. Ina suke lokacin da na sasanta al’ummomin da suke rikici a Kano? Ina suke lokacin da na gina ofishin ‘yan sanda a Dorayi? Ba su yaba da waɗannan ƙoƙarin ba.”

Ya ƙara da cewa ya taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasa sama da 160, yayin da ya ce fiye da matasa da mata 2,000 suka amfana da shirye-shiryen tallafawa jama'a a ƙarƙashin jagorancinsa.

Yan daba: Amnesty ta bukaci daukar mataki

Kara karanta wannan

Yahaya Bello ya san makomarsa, kotu ta yi hukunci kan takararsa ta sanata

Mun ba ku labarin cewa Amnesty International ta yi Allah wadai da harin da wasu ’yan daba suka kai wa tawagar yakin neman zaben PDP a Gombe ranar 11 ga Nuwamba, 2026.

Kungiyar ta ce tana zargin maharan da hannu a jam’iyyar APC, inda ta bukaci jami’an tsaro su gudanar da bincike tare da hukunta wadanda aka samu da laifi.

A daya bangaren kuma. rundunar ’yan sandan Gombe ta tabbatar da faruwar lamarin, amma ta ce ba ta kama wani mutum ba kawo yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.