"Akwai Damuwa game da Abubuwan da ke Faruwa a Najeriya gabanin Zaben 2027"
- Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya nuna damuwa kan yadda siyasar Najeriya ke tafiya gabanin zaɓen 2027
- Ya ce rashin haƙurin siyasa, ta’addancin ’yan daba da amfani da matasa wajen tayar da hankali na barazana ga dimokuraɗiyyar ƙasar
- Jonathan ya buƙaci ’yan Najeriya su fifita ƙwarewa, amana da cancanta wajen zaɓen shugabanni, maimakon la’akari da ƙabila ko addini
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya nuna damuwa kan alkiblar da Najeriya ke bi gabanin babban zaɓen 2027.
Jonathn ya yi gargaɗin cewa ƙaruwar rashin haƙurin siyasa, tashin hankali da hamayyar ƙabilanci na iya yin barazana ga zaman lafiya da kwanciyar hankalin ƙasar.

Source: Twitter
A rahoton Daily Trust, Jonathan ya ce yadda ake gudanar da yaƙin neman zaɓe yana kama da yadda ƙungiyoyin asiri ke tafiyar da harkokinsu, inda ’yan siyasa ba sa son amincewa da ra’ayoyin da suka saɓa da nasu.

Kara karanta wannan
Shugaban APC ya ware gwamnonin Arewa 7, ya ba su shawara kan goyon bayan Tinubu a 2027
Tsohon shugaban ƙasar ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja, yayin wani taron zaman lafiya da tsaro da gidauniyar Goodluck Jonathan Foundation ta shirya.
Jonathan ya koka kan rikicin siyasa
Jonathan ya ce har yanzu yana ci gaba da samun kiraye-kirayen waya daga ’yan Najeriya da abokan ƙasar da ke sassan duniya, waɗanda ke nuna damuwarsu kan yanayin siyasar ƙasar gabanin zaɓen.
“Yayin da muke kara matsawa a hankali zuwa babban zaɓen 2027, wasu abubuwan da ke faruwa a fagen siyasarmu na ƙara zama abin damuwa.
“A matsayina na tsohon shugaban ƙasa, ina samun kiraye-kirayen waya daga ’yan Najeriya da abokan ƙasarmu a sassan duniya, waɗanda ke nuna damuwarsu kan alkiblar da Najeriya ke bi.
“Maimakon ƙwarin gwiwa da fata na alheri da ya kamata mu ƙarfafa a zukatan mutane, ana samun ƙarin fargaba kan yiwuwar rikice-rikicen da za su iya biyo bayan zaɓen. Bai kamata mu yi watsi da waɗannan damuwa ba.”

Kara karanta wannan
Peter Obi ya shirya share hawayen 'yan Arewa, ya gano hanyar magance matsalar yankin
- Dr. Goodluck Jonathan.
Ya soki abubuwan da ke faruwa
Ya bayyana rashin haƙurin siyasa, amfani da ’yan daba da kuma mayar da matasa makamin tada hankula a matsayin wasu manyan barazanar da ke fuskantar tsarin dimokuraɗiyyar ƙasar.
“A bayyane yake cewa wasu ’yan siyasa na ƙin amincewa da ra’ayoyin da suka saɓa da nasu, ko kuma suna kokarin tauye haƙƙin wasu na fafatawa wajen neman mulki.
“Abin yana ƙara bayyana a fili, muna gudanar da ƙungiyoyin siyasa da tawagogin yaƙin neman zaɓe kamar ƙungiyoyin asiri,” in ji shi.

Source: Getty Images
Jonathan ya kuma nuna damuwa kan hukuncin kotuna masu karo da juna, musamman hukuncin da kotunan da suke da matsayi ɗaya ke yankewa, yana mai gargaɗin cewa irin wannan saɓani na iya rage amincewar jama’a ga ɓangaren shari’a.
Dangane da zaɓen shugabanni, ya buƙaci ’yan Najeriya su fifita ƙwarewa, amana da cancanta yayin zaɓen waɗanda za su jagorance su, maimakon barin ƙabila, addini da sauran bambance-bambance su rinjaye su.

Kara karanta wannan
Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro
Jonathan ya bukaci gyara tsarin zabe
Kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan ya ce ci gaban Najeriya zai tsaya cak idan aka ci gaba da amfani da tsohon tsarin zaɓe.
Jonathan ya ce tsarin zaɓen shugabanni da ake amfani da shi a Najeriya yana buƙatar sauyi mai zurfi domin ƙasar ta samu shugabanci nagari da zai iya cimma manufofin ci gabanta.
Asali: Legit.ng