Shugaban FIFA Ya Leƙo Ayyukan Alherin Tinubu, Ya Faɗi Ɓangaren da Ya Yi Fice

Shugaban FIFA Ya Leƙo Ayyukan Alherin Tinubu, Ya Faɗi Ɓangaren da Ya Yi Fice

  • Shugaban FIFA, Gianni Infantino, ya yabawa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan zuba jari wajen inganta kayayyakin more rayuwar wasanni a Najeriya
  • Infantino ya ce gina filayen wasanni na zamani ya nuna yadda Najeriya ta ba matasa muhimmanci tare da shirin samar musu da kyakkyawar makoma
  • Shugaban FIFA ya kuma tabbatar wa Najeriya cewa hukumar za ta ci gaba da tallafa mata, bayan kasar ta goyi bayan neman wa'adin shugabancinsa na gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya yaba wa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa kokarin da take yi wajen bunƙasa kayayyakin more rayuwar wasanni a Najeriya.

Infantino ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin taron babban zauren ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Afirka (CAF) karo na 48 da aka gudanar a Abuja.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Shugaban FIFA ya yabawa Tinubu
Shugaban FIFA, Gianni Infantino yana jawabi ga mutane. Hoto: SOPA Images.
Source: Getty Images

Shugaban na FIFA ya bukaci tawagar Najeriya da ta isar da sakon gaisuwarsa ga Tinubu, tare da jinjinawa shugaban ƙasar da sauran shugabannin Najeriya bisa gudunmawarsu wajen ci gaban wasanni, cewar Vanguard.

Infantino ya yabawa kokarin Tinubu

Ya ce gwamnatin Tinubu tana yin gagarumin aiki wajen inganta wasanni, lamarin da ya nuna cewa Najeriya na da hangen nesa da kuma shirin gina kyakkyawar makoma.

Infantino ya ce jarin da ake zubawa wajen gina da inganta wuraren wasanni ya nuna amincewar Najeriya da irin baiwar da matasanta ke da ita.

Ya kuma yaba wa Shugaban Hukumar Wasanni ta Ƙasa, Shehu Dikko, inda ya ce ya tattauna da shi kan yadda ake bunkasa kayayyakin more rayuwar wasanni a kasar.

A yayin jawabin nasa, Infantino ya gode wa Najeriya bisa kyakkyawar tarbar da aka yi masa da tawagarsa, ciki har da babban sakataren FIFA, Mattias Grafström.

Ya bayyana ziyarar a matsayin wata dama ta sake sada zumunci da nahiyar Afirka, yana mai cewa goyon bayan da Najeriya ke bai wa FIFA na da matuƙar muhimmanci a gare shi.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da kamfen a Najeriya, Tinubu ya gamu da gagarumar koma baya a Arewa

Wannan yabo na zuwa ne bayan ziyarar gani da ido da Infantino ya kai wasu muhimman ayyukan wasanni a Najeriya ranar Juma'a.

An yabawa Tinubu kan ayyukan alheri
Shugaba Bola Tinubu yayin kamfen a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Wuraren da shugaban FIFA ya ziyarta

Daga cikin wuraren da ya ziyarta akwai filin wasa na Warri City Stadium da aka gyara, da kuma ƙaramin filin wasa da cibiyar wasanni ta kwalejin Hussey da ke Delta.

Haka kuma, ya duba aikin gina cibiyar fasaha ta FIFA Forward da ake gudanarwa a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja.

Infantino ya bayyana cibiyar a matsayin wani muhimmin jari da zai taimaka wajen tsara makomar ƙwallon ƙafa a Najeriya, cewar Punch.

Ya ce aikin hadin gwiwa ne tsakanin ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Najeriya da FIFA domin samar da damarmaki ga yara maza da mata masu sha'awar wannan wasa.

A ziyarar da ya kai filin wasan Warri, shugaban FIFA ya jaddada muhimmancin gina ƙananan filayen wasanni domin bai wa al'ummomi damar shiga harkar ƙwallon ƙafa cikin sauƙi.

Gwamna ya rokawa Tinubu alfarma

Mun ba ku labarin cewa Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya ce zai rasa karfin siyasa idan Shugaba Bola Tinubu bai yi nasara a zaben shugaban kasa na 2027 ba.

Kara karanta wannan

Fashola ya fito da bayanin da ya kamata mutane su sani kan yanayin lafiyar Tinubu

Okpebholo ya kwatanta kansa da ’yan kalangu da ke rawa bisa kidan wani, yana mai cewa Tinubu ne ke taimaka masa a siyasance.

Gwamnan ya sake nanata alkawarin samar wa Tinubu kuri'u miliyan 2.5 daga Edo, duk da cewa a 2023 Peter Obi ya lashe jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.