Jerin Kasashe 10 da Ake Hasashen Za Su Fi Yawan Mabiya Addinin Musulunci a Duniya
- Rahoto ya yi hasashen cewa Musulmai za su zarce Kiristoci a matsayin mafi yawan mabiya addini a duniya nan da shekarar 2035
- Ana sa ran Najeriya za ta kasance cikin ƙasashe 10 na farko da suka fi yawan Musulmai a duniya nan da 2070
- Cibiyar Pew Research Center ta yi hasashen cewa yawan Musulman Najeriya zai kai miliyan 282 nan da shekarar 2070
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ana hasashen cewa Musulmai za su zarce Kiristoci a matsayin mafi yawan mabiya addini a duniya nan da shekarar 2035 yayin da ake sa ran Najeriya za ta kasance cikin ƙasashe mafi yawan mabiya addinan biyu nan da shekarar 2070.
Wannan na ƙunshe ne a cikin rahoton da cibiyar bincike ta Pew Research Center ta wallafa a ranar 18 ga watan Nuwamba, 2026, waɗanda suka yi nazari kan hasashen yawan Musulmai da Kiristoci a duniya tsakanin 2020 da 2070.

Source: Getty Images
Punch ta ruwaito cewa rahoton ya nuna cewa yawan Musulmai a duniya zai ƙaru fiye da na sauran addinai, yayin da Kiristanci zai ci gaba da riƙe kusan kaso ɗaya na yawan al’ummar duniya.
Pew ta yi hasashen cewa yawan Musulmai zai ƙaru da kashi 80 cikin 100 tsakanin 2020 da 2070, idan aka kwatanta da ƙarin kashi 11 cikin 100 na mutanen da ba Musulmai ba.
“Musulmai su ne mabiyan addini mafi saurin ƙaruwa a duniya, kuma ana sa ran wannan yanayi zai ci gaba a shekaru masu zuwa,” in ji rahoton da ya yi nazari kan makomar yawan Musulmai a duniya.
Ƙasashen da suka fi yawan Musulmai
A shekarar 2020, Indonesia ce ƙasa mafi yawan Musulmai a duniya, inda take da mabiya miliyan 239, sai Pakistan mai miliyan 227 da Indiya mai miliyan 213.
Bangladesh da Najeriya sun kasance a matsayi na huɗu da na biyar, inda suke da Musulmai miliyan 151 da miliyan 120 bi da bi.
Sai dai ana hasashen cewa nan da shekarar 2070, Pakistan za ta zama ƙasa mafi yawan Musulmai a duniya da miliyan 461, sai Indiya mai miliyan 334 da Najeriya mai miliyan 282.
Ana sa ran Indonesia za ta koma matsayi na huɗu da Musulmai miliyan 274, yayin da Bangladesh za ta kasance ta biyar da miliyan 218.
Ƙasashe 10 mafi yawan Musulmai
Ƙididdigar shekarar 2020
- Indonesia
- Pakistan
- Indiya
- Bangladesh
- Najeriya
- Masar
- Iran
- Turkiyya
- Sudan
- Aljeriya
Hasashen shekarar 2070
- Pakistan
- Indiya
- Najeriya
- Indonesia
- Bangladesh
- Masar
- Habasha
- Sudan
- Turkiyya
- Afghanistan
Pew ta ce ana sa ran Najeriya za ta koma matsayi na uku a duniya wajen yawan Musulmai nan da shekarar 2070, yayin da Habasha da Afghanistan za su shiga cikin ƙasashe 10 mafi yawan Musulmai.
Musulmai za su fi kiristoci yawa
Kun ji cewa wani sabon bincike ya nuna cewa Musulunci na iya zama addini mafi yawan mabiya a duniya, inda zai zarce Kiristanci nan da shekarar 2035.
Binciken ya yi nazari kan ƙasashe da yankuna 201, inda ya yi hasashen sauyin yawan mabiya addinai daban-daban daga 2020 zuwa 2070.
Asali: Legit.ng

