Bayan Hallaka Basarake a Niger, Gwamnati Ta Yi Magana bayan Ɗaukar Matakai

Bayan Hallaka Basarake a Niger, Gwamnati Ta Yi Magana bayan Ɗaukar Matakai

  • Gwamnatin Niger ta tabbatar da mutuwar mutane biyar, ciki har da dagacin garin Lumma Ba’are, bayan wasu mahara sun kai hari a karamar hukumar Borgu
  • Gwamnatin ta ce an tura jami’an tsaro na hadin gwiwa domin dawo da zaman lafiya, yayin da ake kokarin kamo wadanda suka kai harin
  • Rahotannin wasu kafafen yada labarai sun bayyana cewa adadin wadanda suka mutu ya kai 11 a harin da aka kai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Minna, Niger - Gwamnatin jihar Niger ta tabbatar da mutuwar mutum biyar sakamakon wani mummunan hari da wasu mahara suka kai wa al'ummar Lumma Ba’are da ke karamar hukumar Borgu.

Gwamnatin ta bayyana cewa daga cikin mutanen da suka mutu har da dagacin garin, Malam Bawa Muhammad, yayin da wasu mutum biyar suka samu raunuka daban-daban.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yan bindiga sun rutsa sarki da wasu bayin Allah suna cikin Sallah

Gwamnati ta ɗauki mataki bayan kisan basarake
Gwamna Umaru Bago na jihar Niger. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Facebook

Kwamishi and i da wayar da kan jama'a na jihar, Obed Nana, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar.

Ya ce maharan sun kutsa cikin garin ne da misalin karfe 5:00 na safiyar ranar 21 ga watan Nuwamba, 2026, a daidai lokacin da ake fama da rikicin al'umma a yankin.

A cewarsa, an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin New Bussa, inda suke samun kulawar likitoci.

Kwamishinan ya kara da cewa maharan sun kuma kona wasu gidaje a yayin farmakin.

Ya bayyana harin a matsayin abin takaici da rashin kabul, tare da mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu da sauran mazauna yankin.

An tura jami'an tsaro domin kamo maharan

Gwamnatin jihar ta ce an tura jami'an tsaro na hadin gwiwa zuwa yankin domin shawo kan matsalar tsaro da kuma tabbatar da kare rayukan al'umma.

Obed Nana ya ce hukumomin tsaro sun fara kokarin gano wadanda suka kai harin tare da kamo su domin fuskantar hukunci.

Kara karanta wannan

Disamba ta karato: Gwamna ya ware N50,000 ga kowane ma'aikaci a jiharsa

Ya kuma bukaci mazauna yankin su kwantar da hankalinsu, su guji daukar doka a hannunsu, sannan su taimaka wa jami'an tsaro da sahihan bayanai.

Sai dai sanarwar gwamnatin ba ta yi cikakken bayani kan musabbabin rikicin al'ummomin da aka ce yana faruwa a yankin ba, haka kuma ba ta bayyana sunayen sauran wadanda suka mutu ba.

Yan bindiga sun yi barna a Niger
Taswirar jihar Niger da ke fama da yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahotanni sun ce mutum 11 sun mutu

Rahotannin farko da kafafen yada labarai suka wallafa sun nuna cewa adadin wadanda suka mutu a harin ya haura wanda gwamnatin jihar ta tabbatar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mutum 11 ne suka mutu, ciki har da dagacin garin da matarsa.

Haka kuma, jaridar ta ce an sake kai wani hari daban a garin Gada-Oli da ke karamar hukumar Borgu a ranar Asabar, inda aka kashe wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba.

Sai dai kakakin rundunar 'yan sandan jihar Niger, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da mutuwar mutum biyar a harin Lumma Ba’are, yana mai cewa an tura jami'an tsaro yankin.

Jaridar Sahara Reporters ma ta ruwaito cewa akalla mutum 11 ne suka mutu, ciki har da kananan yara ‘yan kasa da shekaru biyar.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun tarwatsa layin wutar lantarki a Najeriya

Rahoton ya kuma yi ikirarin cewa an sace wasu mutane tare da kona gidaje, shaguna da babura a yayin harin.

Yan ta'adda sun lalata wutar lantarki

Mun ba ku labarin cewa wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun tarwatsa ginshikan wutar lantarki guda biyu da ke hada tashar samar da wuta ta Dam din Kainji da Jebba a jihar Neja.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2 na rana a ranar 17 ga Nuwamba, tsakanin al’ummomin Kanti da ke karamar hukumar Mashegu da Kanya a Mokwa.

Rahoton ya ce babu wanda ya rasa ransa, amma fashewar ta jefa mazauna yankunan da ke kusa cikin firgici.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.