Yan Bindiga Sun Turo Sako Za Su Kai Hari Makarantar 'Yan Mata? Gaskiya Ta Fito

Yan Bindiga Sun Turo Sako Za Su Kai Hari Makarantar 'Yan Mata? Gaskiya Ta Fito

  • Shugaban ƙaramar hukumar Zurmi ta Zamfara, Hon. Sama’ila Hussaini Moriki, ya musanta jita-jitar shirin kai hari makarantar sakandaren ’yan mata da ke Moriki
  • Ya bukaci mazauna yankin su kwantar da hankulansu, yana mai cewa jami’an tsaro na nan a yankin
  • Rahoton jita-jitar ya tayar da hankula bayan wasu mazauna Moriki biyu sun yi zargin cewa ’yan bindiga sun sanar da shirin kai hari makarantar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Shugaban ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, Hon. Sama’ila Hussaini Moriki, ya musanta jita-jitar cewa ana shirin kai hari makarantar sakandaren ’yan mata da ke Moriki.

Ya tabbatar wa mazauna Zurmi da daukacin jihar Zamfara cewa jami’an tsaro na da isasshen ƙarfin da za su tabbatar da tsaron yankin.

Gwamnan Zamfara.
Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal a gidan gwamnatinsa da ke Gusau Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

Moriki ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da jaridar Leadership ranar Juma’a, bayan rahotannin cewa ’yan bindiga sun sanar da mazauna Moriki cewa za su kai hari makarantar, sannan an janye jami’an tsaron da aka girke.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Rahoton, wanda wasu mazauna Moriki biyu suka gabatar, ya jawo fargaba a tsakanin al’ummar yankin.

Yan bindiga za su kai hari makaranta?

Da yake musanta jita-jitar, shugaban ƙaramar hukumar Zurmi ya ce ba shi da irin wannan bayani, kuma babu wanda ya taɓa sanar da shi hakan.

“Har zuwa yanzu ba ni da wani bayani a kan hakan, kuma ban taɓa jin irin wannan magana daga wurin wani ba,” in ji Moriki.

Ya ce ya nemi mazauna yankin da suka tayar da ƙararrawar su ba shi lambobin wayar mutanen da ke Moriki domin ya tantance sahihancin zargin, amma suka ƙi, suna masu cewa majiyoyinsu na ɓoye.

Ya buƙaci mazauna yankin su kwantar da hankulansu, kada su firgita saboda rahotannin da ba a tabbatar da sahihancinsu ba, yana mai tabbatar da cewa hukumomin tsaro na nan a Zurmi.

Zurmi na fuskantar hare-haren ’yan bindiga

Garin Moriki da ke ƙaramar hukumar Zurmi ya kasance ɗaya daga cikin wuraren da hare-haren ’yan bindiga suka fi shafa a yankin Arewacin Zamfara.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya je Maiduguri, ya fito da abubuwa 3 da za su sa 'yan Arewa su nemi canji a 2027

A baya, ’yan bindiga sun taɓa kai hari makarantar Government Girls Comprehensive Secondary School da ke Moriki, lamarin da ya ƙara tayar da fargaba a duk lokacin da jita-jitar sabon hari ta yaɗu.

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ƙaramar hukumar Zurmi, wadda ke da iyaka da jihar Katsina da kuma Jamhuriyar Nijar, na cikin ƙananan hukumomin da rikicin ta’addanci ya fi shafa, inda mutanen Moriki, Dauran da wasu ƙauyuka ke fuskantar hare-hare akai-akai.

Shugaban ƙaramar hukumar, wanda kuma shi ne shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) a jihar Zamfara, ya dage cewa Zurmi na cikin aminci, tare da kira ga jama’a da su yi watsi da jita-jitar da za ta iya tayar da hankula.

Yan bindiga sun kai hari masallaci

Kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari kan masallaci yayin sallar Asuba a garin Kaura, da ke karamar hukumar Kaura-Namoda a jihar Zamfara.

Rahoton da aka samu ya nuna cewa maharan sun kashe mutum guda da aka ce hadimin gwamnan Zamfara da ake kira Nasiru Sani Kaura ne tare da yin garkuwa da wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262