Manyan Labarai A Yau
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, ya rubuta wasika ga hukumar PSC domin neman a yi wa wasu 'yan sanda karin girma na musamman.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar dakile wani hari na 'yan ta'addan Boko Haram/ISWAP a jihar Borno. Sojojin sun kashe 'yan ta'adda da dama.
Shugaban Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya sallami Firaminista Ousmane Sonko tare da rusa gwamnati bayan watanni ana rikicin siyasa da matsin tattalin arziki.
Babbar kotun tarayya ta Najeriya ta tabbatar da rasuwar daya daga cikin alkalanta, Mai Shari'a Mohammed Yunusa bayan ya yi wata faduwa a cikin gidansa.
Tsohon Ministan harkokin waje, Ambassada Yusuf Tuggar, ya sha kasa bayan da jam'iyyar APC ta sanar da sakamakon zaben fitar da gwani na gwamnan jihar Bauchi.
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa zai gudanar da ayyukan da za su amfani 'yan Najeriya idan ya samu nasarar zama shugaban kasa.
Tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa ya taka muhimmiyar rawa wajen samun nasarar tsohon shugaban kasa, marigayi Muhammadu Buhari.
Shugabar hukumar leken asirin Amurka, Tulsi Gabbard, ta yi murabus daga kan mukaminta. Tulsi Gabbard ta bayyana cewa ta dauki matakin ne domin kula da wani abu.
Shugaban Majalisar dokokin jihar Kwara, Rt. Hon Salihu Yakubu Danladi ya zama dan takarar gwamnan APC a zaben jihar na 2027 bayan lashe zaben fitar da gwani.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari