Tinubu Ya Sake Dawo da Alkawarin da Ya Dauka a Baya, Ya Roki Yan Najeriya

Tinubu Ya Sake Dawo da Alkawarin da Ya Dauka a Baya, Ya Roki Yan Najeriya

  • Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta inganta samar da wutar lantarki a faɗin ƙasar
  • Tinubu ya sanar da yarjejeniyar da aka kulla da kamfanin Yutong na China domin farfaɗo da tsohon kamfanin haɗa motoci
  • Shugaban ƙasar ya kuma yi jimamin mutuwar mutane huɗu a hatsarin kwale-kwale a Bayelsa, tare da shirin ziyarar ta'aziyya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ’yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta inganta samar da wutar lantarki.

Tinubu ya bayyana cewa ƙoƙarin faɗaɗa masana’antu da jawo masu zuba jari zai kawo sauyi a ɓangaren wutar lantarki.

Tinubu ya yi alkawarin samar da wutar lantarki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yana jawabi. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Alkawarin da Tinubu ya yi

Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin taron gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC a Ibadan, jihar Oyo, cewar The Nation.

Kara karanta wannan

Abin mamaki da Kwankwaso ya leko a Arewa maso Gabas kan takararsa da Obi

Ya kuma sanar da sabuwar yarjejeniya da katafaren kamfanin kera motoci na China, Yutong, domin farfaɗo da tsohon kamfanin haɗa motoci na Leyland.

Ya ce:

“Yayin da muke ci gaba da kawo masana’antu, za ku gani, kuma ina tabbatar muku da cewa za a samu ingantuwar wutar lantarki.”

Shugaban ya bayyana kwarin gwiwarsa kan ƙoƙarin waɗanda ke taimakawa wajen jawo masu zuba jari a masana’antu, musamman Ministan Wutar Lantarki, Joseph Tegbe, da tawagarsa, waɗanda ya yaba wa ƙoƙarinsu.

Wannan tabbaci na zuwa ne a daidai lokacin da ’yan Najeriya ke ƙara buƙatar ingantacciyar wutar lantarki domin tallafa wa kasuwanci, masana’antu da bukatun gidaje a faɗin ƙasar nan, cewar Tribune.

Tinubu ya yi irin wannan alƙawari a ranar 10 ga watan Nuwamba yayin gangamin APC a Dutse, jihar Jigawa, inda ya ce gwamnatinsa za ta bi wata sabuwar hanya wajen magance matsalar wutar lantarki da ta daɗe tana addabar ƙasar.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa ta ɓullo, ana zargin wasu mutane na yaudarar Tinubu gabanin zaben 2027

Za a samar da ingantacciyar wuta a Najeriya
Ministan makamashi a Najeriya, Joseph Tegbe. Hoto: Federal Ministry of Power.
Source: Twitter

Alkawarin da Tinubu a Oyo

Dangane da jihar Oyo kuwa, shugaban ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kammala yarjejeniya da kamfanin Yutong na China domin farfaɗo da ayyukan haɗa motoci a tsohon kamfanin Leyland da ke Ibadan.

Ya ce:

“A jihar ku, mun kammala sanya hannu kan yarjejeniya da Yutong na China domin sake buɗe tsohon kamfanin Leyland da ke Ibadan, wanda yake da masana’antar haɗa motoci.”

Yarjejeniyar na daga cikin shirin gwamnatin tarayya na samar da motocin sufuri masu amfani da iskar gas mai matsewa (CNG) a farashi mai sauƙi, inda ake sa ran Yutong zai samar da motocin bas 300 a matakin farko.

Halascin da Arewa ta yi wa Tinubu

Kun samu labarin cewa ɗan jarida Simon Kolawole ya ce tasirin yan Arewa ne ya hana Shugaba Bola Tinubu shan kaye a zaɓen 2023.

Kolawole ya bayyana cewa kashi 39 cikin 100 na ƙuri’un Arewa sun tafi ga Tinubu, yayin da Atiku Abubakar ya samu kashi 36.

Ya ce alaƙar siyasar Tinubu a Arewa, biyayya ga jam’iyyu da rarrabuwar kawunan ’yan adawa sun taimaka wajen nasararsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.