Matsala na Neman Tunkaro Atiku kan Zaben 2027, Kungiya Ta Mika Bukatunta

Matsala na Neman Tunkaro Atiku kan Zaben 2027, Kungiya Ta Mika Bukatunta

  • Ƙungiyar NUF ta bukaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yi ritaya daga siyasa, tana mai cewa ya kamata matasa su karɓi ragamar shugabanci
  • Ƙungiyar ta zargi Atiku da gazawa wajen kawo ci gaba a Arewa maso Gabas, duk da shekaru takwas da ya yi a matsayin mataimakin shugaban ƙasa
  • NUF ta kuma yi nuni da wasu zarge-zargen da suka shafi Atiku, tare da nuna damuwa kan rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar ADC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ƙungiyar North East Unity Forum (NUF) ta bukaci tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya hakura da burinsa na neman shugabancin Najeriya a zaɓen 2027, tare da yin ritaya daga siyasa.

Ƙungiyar ta bayyana cewa Najeriya na buƙatar shugabanni matasa masu kuzari da sabbin dabarun tafiyar da ƙasa, maimakon ci gaba da dogaro da tsofaffin ’yan siyasa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya gamu da gagarumar matsala a cikin APC kan shirinsa na tazarce a 2027

Kungiya na son Atiku ya yi ritaya
Atiku Abubakar na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

A cewar ƙungiyar, Atiku, wanda ke gab da cika shekara 80, ba shi da kuzarin jiki, sabbin dabaru da kuma mutuncin da ake buƙata wajen jagorantar ƙasa a wannan zamani mai saurin sauyawa, cewar rahoton jaridar The Nation.

A cikin wata sanarwa da mai gudanar da ayyukan ƙungiyar na ƙasa, Comrade Bukar Mustapha, ya sanya wa hannu, NUF ta lissafa abin da ta kira gazawar Atiku a fannonin siyasa, tattalin arziki da ci gaban al’umma.

Ta ce duk da tsawon shekarun da ya yi yana riƙe da muƙaman gwamnati, bai kawo sauyin da ake buƙata a yankin Arewa maso Gabas ba.

NUF ta ce Atiku ya tsufa a siyasa

Ƙungiyar ta bayyana Atiku a matsayin ɗaya daga cikin tsofaffin ’yan siyasa da suka daɗe suna mamaye harkokin siyasar Najeriya ba tare da samar da sakamakon da ake buƙata ba.

Ta ce shugabancin zamani na buƙatar kuzari, saurin fahimta da sabbin dabaru, tana mai cewa matasan Najeriya na ƙara buƙatar sauyin zamani a shugabanci.

Kara karanta wannan

Kotu ta kawo cikas ga yunkurin Atiku na neman hana Tinubu yin takara a 2027

NUF ta lura cewa Atiku ya kasance fitaccen ɗan siyasa tun shekarar 1993, amma har yanzu ba ta ga irin shugabancin sauyi da take ganin zai iya ciyar da ƙasar gaba ba.

Ƙungiyar ta kuma yi tambaya kan gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Arewa maso Gabas, duk da kasancewarsa ɗan yankin da kuma shekaru takwas da ya yi a matsayin mataimakin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo.

Ta bayyana rashin gina hanyar da za ta kai zuwa garin Atiku a matsayin abin takaici, duk da irin ƙarfin tasirin siyasar da yake da shi a lokacin.

Haka kuma, ta zarge shi da rashin ba matasan yankin jagoranci, tallafi da damar samun ci gaba yadda ya kamata.

A cewar ƙungiyar, Arewa maso Gabas na buƙatar shugabanni da za su fifita ci gaban yankin, ba waɗanda ke tuna asalinsu ne kawai a lokacin yaƙin neman zaɓe ba.

An yi tambayoyi kan tarihin Atiku a fannin tattalin arziki

A fannin tattalin arziki, NUF ta yi zargin cewa lokacin da Atiku ya kasance mataimakin shugaban ƙasa ya yi daidai da koma bayan wasu manyan masana’antun cikin gida da kuma ƙarin dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.

Kara karanta wannan

Fadan manya: Bayan karyata shi, Sule Lamido ya sake taso Kashim Shettima a gaba

Ta kuma yi tambaya kan yadda ya gudanar da shirin sayar da kadarorin gwamnati ga masu zaman kansu, tana zargin cewa wasu daga cikin yarjejeniyoyin sun fi amfanar da wasu tsirarun masu ƙarfin iko maimakon ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa.

Ƙungiyar ta kuma ambaci wasu batutuwan da suka taɓa tayar da ce-ce-ku-ce game da Atiku, ciki har da zargin biyan dala 500,000 da ke da alaƙa da aikin samar da wutar lantarki na Mambilla da tsohuwar matarsa.

Ta kuma yi nuni da badakalar cin hanci da ake dangantawa da kamfanin Siemens, da kuma binciken da Majalisar Dattawan Amurka ta gudanar kan sama da dala miliyan 40 na kuɗaɗen da ake zargi da kasancewa na shakku.

NUF ta ce waɗannan batutuwa na haifar da tambayoyi kan dacewar Atiku ya jagoranci harkokin ƙasar, musamman wajen kula da kuɗaɗen gwamnati.

Ƙungiyar ta yi magana kan rikicin ADC

NUF ta kuma nuna damuwa kan rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Ta ce hukuncin da wata babbar kotun tarayya ta yanke ya jefa tsarin shugabancin jam’iyyar da kuma sahihancin tsarin da ya samar da takarar Atiku cikin rashin tabbas.

Bisa waɗannan dalilai, ƙungiyar ta shawarci tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ya hakura da burinsa na takarar shugaban ƙasa, ya kuma more ritayarsa a Najeriya ko Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), inda take cewa yakan kai ziyara akai-akai.

Kara karanta wannan

Tsohon na kusa da Atiku ya zayyano matsalolin dan takarar na ADC a 2027

Ta ce ’yan Najeriya sun gaji da ’yan siyasar da take kira ’yan kasuwar siyasa, waɗanda ke ci gaba da neman muƙaman zaɓe ba tare da gabatar da sabbin hanyoyin magance matsalolin ƙasar ba.

Ƙungiyar ta jaddada cewa Arewa maso Gabas na buƙatar sabon ƙarni na shugabanni da za su mayar da hankali kan magance matsalolin ci gaban yankin, maimakon ci gaba da dogaro da ’yan siyasar da suka shafe shekaru da dama suna riƙe da manyan muƙamai.

Atiku ya samu kira daga wajen kungiyar NUF
Atiku Abubakar a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Twitter

Kotu ta yi watsi da bukatar Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yi watsi da bukatar Atiku Abubakar, na gabatar da sababbin hujjoji a ƙarar da ya shigar domin neman hana Shugaba Bola Tinubu tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027.

Ƙarar ta shafi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu ya yi amfani da takardar shaidar kammala bautar ƙasa ta NYSC ta bogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng