Shugaban Obidients Ya Tabo Batun Peter Obi Ya 'Rusa' Masallaci Lokacin da Yake Gwamna
- An yada wasu maganganu kan zargin cewa Peter Obi ya rusa masallaci lokacin da yake kan madafun ikon jihar Anambra
- Shugaban kungiyar Obidient Movement, Yunusa Tanko, ya fito ya yi magana kan zargin wanda aka yada a kan dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC
- Yunusa Tanko ya bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen wanke Peter Obi daga abubuwan da ake danganta shi da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Shugaban kungiyar Obidient Movement, Yunusa Tanko, ya yi watsi da zargin cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar NDC, Peter Obi, ya rushe masallaci a lokacin da yake gwamnan jihar Anambra.
Yunusa Tanko ya jaddada cewa iƙirarin ƙarya ne kuma babu wata shaidar da ke akwai da ke goyon bayansa.

Source: Facebook
Shugaban na kungiyar Obedient Movement ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Litinin, 6 ga watan Yunin 2026.
Yunusa Tanko ya kare Peter Obi
Yunusa Tanko ya ce bayanai na tarihin lokacin mulkin Peter Obi suna nuna cewa tsohon gwamnan na Anambra ya kiyaye kyakkyawar dangantaka da al'ummar Musulmi kuma ya tallafa wa ginin masallaci a jihar.
Shugaban na Obidient Movement ya ce ƙungiyar za ta ci gaba da ƙalubalantar abin da ya bayyana a matsayin karkatar da labari da kuma ƙoƙarin ganganci na ɓata tarihin Obi a lokacin da yake kan muƙamin gwamnati.
“Za mu ci gaba da karyata zargin ƙarya da ake yi wa Mai girma Peter Obi. Tun daga iƙirarin cewa ya rushe masallaci, alhali shaidu sun nuna cewa ya tallafa kuma ya gina guda ɗaya, har zuwa ga karkatar da labari dake tattare da batun katin shaida, za mu ci gaba da gabatar da gaskiyar lamarin.”
- Yunusa Tanko
'Yan Obidient za su ci gaba da kare Obi
Ya tabbatar da cewa ƙungiyar ba za ta yi shuru ba yayin da ake fuskantar karairayi da ta yi amannar suna da nufin ɓata sunan Obi gabannin babban zaɓen shekarar 2027.
A cewarsa, ƙungiyar ta Obidient Movement tana ci gaba da kasancewa mai jajircewa wajen gabatar da bayanan gaskiya da kuma gyara kalaman da take ɗauka a matsayin masu kawo rudani.

Source: Facebook
“Kamar yadda muka saba yi a kowane lokaci, za mu ƙalubalanci ƙaryace-ƙaryace kuma za mu fallasa kowane ƙoƙari na mugunta da nufin ɓata amincinsa da mutuncinsa."
“Gaskiya tana nan daram, kuma babu wani adadi na farfaganda da zai iya sauya ta. Sabuwar Najeriya tana yiwuwa, kuma Najeriya za ta zama OK”
- Tunusa Tanko
Peter Obi ya magantu kan Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NDC a zaben 2027, Peter Obi, ya yi magana kan Atiku Abubakar.
Peter Obi Obi ya musanta rade-radin cewa yana guje wa Atiku Abubakar gabanin zaben 2027 da ake tunkara bayan barin jam'iyyar ADC zuwa NDC.
Obi ya ce bai taba gudun Atiku ko wani mutum ba, yana mai jaddada cewa salon tafiyar siyasarsa ne kawai ya bambanta da na wasu.
Asali: Legit.ng

