Jagoran 'Yan Bindiga da Suka Sace Tsohon Janar a Katsina Ya Mika Bukatunsa ga Gwamnati
- An samu labarin cewa 'yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar Rabe Abubakar (mai ritaya)
- Jagoran 'yan bindigan da suka yi garkuwa da tsohon Janar din tare da matarsa ya tuntubi iyalansa bayan sace shi
- Majiyoyi sun bayyana cewa Kachallah Muhammad ya mika bukatarsa ga gwamnati ta hannun iyalan tsohon sojan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Wani shahararren shugaban ’yan bindiga, Kachallah Muhammad, ya tuntuɓi 'yan uwan tsohon babban jami'an soja da aka sace, Manjo Janar Rabe Abubakar Batsari.
Jagoran 'yan bindigan ya tuntubi iyalan tsohon sojan ne domin mika bukatar da yake son a cika masa.

Source: Twitter
Majiyoyi sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa jagoran 'yan bindigan wanda ke gudanar da ayyukansa a sassan jihar Katsina, ya buɗe hanyar sadarwa da iyalin tsohon Janar ɗin a safiyar ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2026.
An ruwaito cewa 'yan bindiga sun sace tsohon Manjo Janar ɗin da mai ɗakin sa ne a ranar Asabar a jihar Katsina.
An yi magana da tsohon Janar
Wani babban jami'i a ƙaramar hukumar Batsari, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya tabbatar da cewa ya tattauna da tsohon sojan da aka sacen da kansa a lokacin tattaunawarsu wadda jagoran 'yan bindigan ya shirya.
“Na yi magana da Manjo Janar Rabe ta hanyar Kachallah Muhammad. Ya shaida mana cewa yana cikin ƙoshin lafiya da ƙarfin jiki, kuma mai ɗakin sa ma tana cikin ƙoshin lafiya."
A cewar majiyar, tsohon janar ɗin ya tabbatar wa iyalansa da abokan arziƙinsa cewa ana kula da su yadda ya dace daga ɓangaren waɗanda suka sace su, wani ci gaba da ya ɗan rage fargaba da damuwa a tsakanin 'yan uwa da mazauna yankin.
Wace bukata jagoran 'yan bindiga ya nema?
Jami'in ya ƙara bayyana cewa a lokacin tattaunawar, Kachallah Muhammad ya bayyana buƙatunsa a fili, inda ya jaddada buƙatar sakin 'yan uwansa, waɗanda ake zargin hukumomin tsaron Najeriya suna tsare da su.
“Ya ce abin da yake so shi ne a saki 'yan uwansa cikin gaggawa waɗanda ke tsare a hannun gwamnati." A cewar jami'in.

Source: Original
Majiyar ta ce jagoran 'yan bindigan ya kuma nuna shirinsa na komawa kan teburin tattaunawa, inda ya nuna cewa a shirye yake ya yi sulhu da nufin dawo da zaman lafiya a Matazu da sauran yankunan da yake da tasiri a kansu.
“Ya ce a shirye yake ya koma kan teburin tattaunawa domin samun zaman lafiya a Matazu da maƙwabtan kauyuka.” in ji jami'in.
'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka mutane da dama bayan kai harin ta'addanci a jihar Sokoto.
'Yan bindigan sun hallaka akalla mutane 17 ciki har da baki masu yawon sallah a wani mummunan hari da suka kai a wani kauye.
Tsagerun 'yan bindigan sun kashe mutanen ne a wani hari da suka kai a kauyen Dangulbi a karamar hukumar Tureta ta jihar Sokoto.
Asali: Legit.ng

