Hayatu Deen: Wanda Ya Fafata da Atiku a ADC Ya Yi Maganar zuwa Kotu don Kalubalantar Zaben
- Mohammed Hayatu-Deen ya yi tsokaci kan zaben fitar da gwani na shugaban kasa na jam'iyyar ADC
- Mai neman takarar shugaban kasar ya bayyana cewa ya hakura da zuwa kotu domin kalubalatar sakamakon zaben
- Hayatu-Deen ya bayyana dalilin da ya sanya ya dauki matakin kin zuwa kotu duk da rashin amincewar da ya nuna da farko
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mai neman takarar shugaban ƙasa na ADC, Mohammed Hayatu-Deen, ya yi magana kan zaben fitar da gwani na jam'iyyar.
Mohammed Hayatu-Deen ya sanar da cewa ba zai ƙalubalanci sakamakon zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa na jam'iyyar da aka gudanar ranar 25 ga watan Mayu, 2026 a kotu ba.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa ta bayan zaɓen fitar gwanin da ya fitar a shafinsa na X a ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2026.
Hayatu-Deen ya hakura da zuwa kotu
Hayatu-Deen ya ce ya yi nazari sosai kan abubuwan da suka faru game da zaɓen fitar da gwanin kuma ya kammala da cewa kiyaye haɗin kan 'yan adawa ya fi muhimmanci fiye da bin sawun matakin shari'a.
Tsohon mai burin takarar shugabancin ƙasar ya nuna rashin gamsuwarsa a baya game da rahotannin tafka magudi na ƙuri'u a tsarin zaɓen fitar da gwanin.
Sai dai kuma, a cikin sanarwarsa ta baya-bayan nan, Hayatu-Deen ya bayyana cewa bayan gudanar da shawarwari masu zurfi, ya yanke shawarar kada ya ƙalubalanci sakamakon a kotu.
Meyasa ya fasa zuwa kotu?
“Na yanke shawara, bayan kyakkyawan nazari da shawarwari masu zurfi, cewa ba zan ƙalubalanci sakamakon zaɓen a kotu ba."
"Najeriya tana buƙatar ’yan adawa masu ƙarfi, inganci, da haɗin kai cikin gaggawa. Wannan manufa dole ne ta kasance mafi girma a kowane lokaci fiye da burin mutum ɗaya ko kuma baƙin cikin siyasa na ɗan lokaci."
- Mohammed Hayatu-Deen
Hayatu-Deen ya bayyana cewa shawarar tasa ta ginu ne a kan babban buri na ƙarfafa hukumomin dimokuraɗiyya da kuma samar da kyakkyawan tsarin siyasa na daban wanda ke da ikon tunkarar ƙalubalen Najeriya.
Yayin da yake waiwayar tafiyarsa ta siyasa, ya tuno shigarsa harkokin siyasar jam'iyya a shekarar 2022 lokacin da ya nemi tikitin shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP.

Source: Twitter
Hayatu-Deen ya yi godiya
Ya ce wannan gogewa ta tsara abubuwan da yake tsammani kuma ta ba shi hasken shiga jam'iyyar ADC, wadda ya yi amannar cewa tana ba da damar gina hamayya mai ƙa'ida wadda ta ginu a kan gaskiya, dimokuraɗiyya ta cikin gida, da kuma sabunta ƙasa.
Hayatu-Deen ya kuma nuna godiyarsa ga magoya baya, masu ba da gudunmawa, ƙwararru, ɗalibai, ma'aikata, da kuma mambobin jam'iyyar amintattu a faɗin ƙasa baki ɗaya saboda jajircewarsu a duk tsawon lokacin yaƙin neman zaɓen.
Atiku ya tattauna da Amaechi
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Atiku Abubakar, ya gana da Rotimi Amaechi.
Atiku Abubakar wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaben 2027, ya ce tattaunawar tasu ta fi mayar da hankali kan halin da Najeriya ke ciki.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa shi da Amaechi sun kuma duba rawar da ‘yan Najeriya masu kishin kasa za su taka wajen nemo mafita daga matsalolin da ake fama da su a kasar nan.
Asali: Legit.ng


