'Yan Bindiga Sun Kai Harin Ta'addanci a Sokoto, an Kashe Masu Yawon Sallah

'Yan Bindiga Sun Kai Harin Ta'addanci a Sokoto, an Kashe Masu Yawon Sallah

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci wanda ya jawo asarar rayukan wasu bayin Allah a jihar Sokoto
  • Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba bayan sun yi dirar mikiya a wani kauye
  • Daga cikin mutanen da 'yan bindigan suka hallaka har da wadanda suka je yawon Sallah amma harin ya ritsa da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Akalla mutane 17, ciki har da baƙi masu yawon Sallah guda bakwai, ne aka kashe biyo bayan wani muna-munan harin 'yan bindiga a jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun kashe mutanen ne a wani hari da suka kai a kauyen Dangulbi a karamar hukumar Tureta ta jihar Sokoto.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Mazauna yankin sun shaida wa jaridar Daily Trust cewa maharan sun kai harin ne a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2026.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda fiye da 20 sun bakunci lahira da sojojin Amurka suka sake kawo dauki Najeriya

'Yan bindiga sun yi barna a Sokoto

'Yan bindigan ɗauke da manyan makamai na zamani kuma a kan babura kusan 150, sun buɗe wa mazauna ƙauyen wuta, suka kwashe kayan shaguna, sannan suka tilasta wa mutane da dama guduwa zuwa daji na kusa.

Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya yi zargin cewa tun da farko 'yan bindigan sun taso ne daga ƙauyen Bagega da ke karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

A cewarsa, maharan sun ratsa ta Barayar Zaki a maƙwabciyar karamar hukumar Bukkuyum kafin su isa ƙauyen Gizazza, inda aka ruwaito cewa sun kwana a can kafin su ƙaddamar da harin.

“Mun samu labarin zirga-zirgarsu a ranar Asabar. Sun fito ne daga Bagega kuma suka ratsa ta Barayar Zaki kafin su isa Gizazza. Mafi yawan lokuta, duk lokacin da suke son kai hari kauyukanmu, suna kwanan dare ne a can sannan su ƙaraso a washe gari."

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: 'Yan sanda sun cafke tantirin jagoran 'yan bindiga a Zamfara

- Wata majiya

Yadda 'yan bindiga suka kai harin

Majiyar ta ce 'yan bindigan sun shiga ƙauyen Dangulbi ne tsakanin ƙarfe 10:00 na safe zuwa ƙarfe 11:00 na safe na ranar Lahadi, kuma nan take suka fara harbi ba kakkautawa.

“Suna isowa suka fara harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba. Mutane sun gudu ta kowane bangare domin neman tsira, amma an kashe mutane 17 a lokacin harin."

- Wata majiya

An bayyana sunayen wasu daga cikin wadanda abin ya shafa da suka haɗa da Munde, Nagoma, Abdullahi, Danbala, Munden Chana, Muhammadu Dan Amo, Hassan, Abubakar Danbaba, da kuma Yidi Bafillace.

'Yan bindiga sun kai hari a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An kashe masu yawon Sallah

Mazauna ƙauyen sun ce biyar daga cikin wadanda abin ya shafa baƙin yawon Sallah ne daga Adarawa, karamar hukumar Gummi ta jihar Zamfara, yayin da wasu mutane biyu kuma baƙi ne daga Gidan Gambo a karamar hukumar Shagari, wanda hakan ya sanya jimillar adadin baƙin da aka kashe a harin ya kai bakwai.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe kansila da babban darakta a Zamfara kwanaki 10 da sace su

Ya ƙara yin zargin cewa maharan sun kwashe tsawon sa'o'i da dama a cikin kauyen bayan karkashe mutanen, kuma sun hana mazauna yankin gudanar da jana'iza da binne wadanda suka mutun.

'Yan bindiga sun kashe kansila

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun hallaka wasu jami'an gwamnati a jihar Zamfara.

Tsagerun 'yan bindigan sun kashe wani kansila da wani darakta na karamar hukumar Talata Mafara a Zamfara bayan sun sace su.

Kisan da suka yi wa mutanen ya biyo bayan kin karbar kudin fansa da aka ba su domin sakin su bayan kwanaki 10 da sace su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng