An Shiga Jimami da 'Yan Bindiga Suka Kashe Basarake Mai Daraja a Plateau
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun sanya mutane cikin jimami a jihar Plateau bayan da suka hallaka wani basarake har lahira
- Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka basaraken ne har lahira bayan sun ritsa shi a hanya lokacin da yake shirin komawa gida
- Shugaban karamar hukumar da lamarin ya auku ya sha alwashin zakulo mutanen da ke da hannu a kisan da aka yi wa basaraken
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Plateau - 'Yan bindiga sun hallaka basaraken garin Timshat da ke karamar hukumar Langtang ta Kudu a jihar Plateau, Godwin Vonga.
Barasaken riga mu gidan gaskiya ne bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe shi a kan hanyar Timshat zuwa Mabudi.

Source: Twitter
Jaridar Premium Times ta ruwaito cewa an kai wa Godwin Vonga, wanda tsohon kansila ne mai wakiltar mazabar Nasarawa a Langtang ta Kudu, hari ne a ranar Lahadi, 31 ga watan Mayun 2026.
'Yan bindiga sun kashe basarake
'Yan bindigan sun farmake shi ne lokacin da yake kan hanyarsa ta komawa gida bayan ya sauke yayansa a makaranta da ke Mabudi.
Mazauna yankin sun ce kisan ya jefa garin Timshat da al'ummomin da ke kewaye da shi cikin jimami da makoki.
Wani mazaunin yankin, Nanbol Pirfa, ya bayyana mamacin a matsayin basaraken gargajiya mai kima da daraja kuma tsohon ma'aikacin gwamnati.
A cewarsa, yanayin da ke tattare da yadda harin ya faru wanda ya yi sanadiyyar kashe basaraken har yanzu ba a tantance shi ba.
Shugaban karamar hukuma ya sha alwashi
Shugaban karamar hukumar Langtang ta Kudu, Nanfa Nbin, ya yi tir da kisan inda ya bayyana shi da cewa aikin dabbanci ne kuma abin da ba za a amince da shi ba a cewar Punch.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Butko Iliya, ya sanya wa hannu, shugaban ya miƙa ta'aziyyarsa ga iyalan mamacin, mutanen Timshat, da kuma daukacin mazauna Langtang ta Kudu.

Kara karanta wannan
'Yan ta'adda fiye da 20 sun bakunci lahira da sojojin Amurka suka sake kawo dauki Najeriya
Mista Nbin ya sha alwashin cewa za a gano waɗanda ke da hannu a kisan kuma za a mika su gaban shari'a domin su fuskanci hukunci.
Ya kuma buƙaci mazauna yankin da su ba da haɗin kai ga hukumomin tsaro ta hanyar ba da bayanan da za su iya taimakawa binciken da ake gudanarwa a halin yanzu.
Shugaban ya yi gargaɗi ga ɓata-gari masu gudanar da ayyukan laifi a cikin ƙaramar hukumar da su nesanta kansu daga ayyukan sabawa doka, idan kuma ba haka ba za su fuskanci cikakken hukuncin doka.

Source: Original
'Yan bindiga sun kai hari a masallaci
A wani labarin kuma, kun ji cewa ‘yan bindiga sun kai hari wani masallaci da ke kauyen Unguwan Namama a yankin Kaya, karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna.
Maharan wadanda ke dauke da makamai sun kashe mutum guda tare da yin garkuwa da wasu masu ibada da ba a tantance adadinsu ba.
Majiyoyi sun nuna cewa 'yan bindigan sun shiga kauyen ne da misalin karfe 7:30 na yammaci, sannan suka nufi masallacin kai tsaye a lokacin da al’umma ke gudanar da sallar Magariba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
