Gwamna Namadi Ya Dakatar da Wasu Hadimansa, an Ji Dalili

Gwamna Namadi Ya Dakatar da Wasu Hadimansa, an Ji Dalili

  • Wasu daga cikin hadiman gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, sun fuskanci dakatarwa ba tare da bata lokaci ba
  • Gwamna Umar Namadi ya ba da umarnin dakatar da hudu daga cikin hadimansa har sai baba ta gani bisa wasu zarge-zarge
  • A cikin sanarwar da aka fitar kan dakatarwar, an bayyana cewa matakin da gwamnan ya dauka zai fara aiki ne ba tare da bata lokaci ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya dauki matakin ladabtarwa kan wasu daga cikin hadimansa.

Gwamna Namadi ya umarci da a dakatar da hudu daga cikin masu taimaka masa na siyasa har zuwa wani lokaci da ba a kayyade ba, kuma matakin ya fara aiki nan take.

Gwamna Umar Namadi ya dakatar da wasu hadimansa
Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi a ofis Hoto: Umar Namadi
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce wannan umarni yana ƙunshe ne cikin wata sanarwar gwamnati da aka fitar ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2026 wadda sakataren gwamnatin jihar, Bala Ibrahim, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

"Da ban kai labari ba"; Gwamna Mutfwang ya fadi abubuwan da suka sa ya samu nasara a Plateau

An dakatar da hadiman Gwamna Namadi

An raba sanarwar ga manema labarai a garin Dutse ta hannun jami'in hulɗa da jama'a na ofishin sakataren gwamnatin jiha (SSG), Ismaila Dutse, jaridar The Nation ta kawo rahoton.

Wani bangare na sanarwar na cewa:

“Dakatarwar ta fara aiki ne nan take."

Hadiman gwamnan da abin ya shafa sun haɗa da Abbas Makama, babban mataimaki na musamman kan kula da ambaliyar ruwa I, Salisu Muhammad, wanda aka fi sani da Rosy Auyo, mataimaki na musamman kan Harkokin kasuwanci.

Sauran su ne Ibrahim Yunusa, mataimaki na musamman kan sanya ido a fannin ilmi a matakin fari III; da kuma Umar Abdulkadir, wanda aka fi sani da Alhaji Bullet Auyo, mataimaki na musamman kan noma.

Meyasa aka dakatar da hadiman?

Sai dai kuma, sanarwar ba ta bayyana kowane irin dalili na dakatar da su ba.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa matakin yana iya samun alaƙa da zargin ayyukan zagon ƙasa ga jam'iyya.

Kara karanta wannan

Tinubu: "Yadda muka ceto Najeriya daga rugujewa a shekaru 3 na mulkina"

Hakazalika a ranar Litinin, jam'iyyar APC reshen Jigawa ta dakatar da wani mamban Majalisar wakilai mai wakiltar mazabar tarayya ta Hadejia/Auyo/Kafin Hausa tare da wasu jami'an jam'iyyar guda shida.

Gwamna Namadi ya dakatar da wasu hadimansa
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa Hoto: Garba Muhammad
Source: Facebook

An dakatar da su saboda zargin halayyar zagon ƙasa ga jam'iyyar biyo bayan zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar.

Sai dai, gwamnatin jihar ko kuma hadiman da abin ya shafa ba su tabbatar a hukumance cewa akwai wata alaƙa tsakanin wannan dakatarwa da kuma siyasar jam'iyyar.

Gwamna Namadi ya hango nasarar Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi, ya hango nasarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Gwamnan Umar Namadi, ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu gagarumar nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Umar Namadi ya bugi kirjin cewa babu wani ɗan adawa, har da tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, da zai iya kawo barazana ga jam’iyyar APC a zaben shekarar 2027 da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng