"Za a Iya Gano Su"; Buratai Ya Dauko Batun 'Yan Bindigan da ke Fitowa a Bidiyoyi

"Za a Iya Gano Su"; Buratai Ya Dauko Batun 'Yan Bindigan da ke Fitowa a Bidiyoyi

  • Ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda 'yan bindiga ke dora bidiyoyinsu a shafukan sada zamunta ba tare da jami'an tsaro sun zakulo su ba
  • Tsohon babban hafsan sojojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya) ya nuna cewa bai yarda jami'an tsaro ba za su iya gano 'yan bindigan ba
  • Tsohon jakadan na Najeriya a kasar Benin ya bayyana cewa hukumomin tsaro suna da cikakkiyar damar bin sawun mutanen da ke aikata laifuffuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon babban hafsan sojojin kasa, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya), ya yi magana kan matsalar 'yan bindiga.

Buratai ya nuna shakku kan iƙirarin cewa hukumomin tsaro ba za su iya gano inda 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane suke ba, waɗanda ke fitowa fili suna yada bidiyoyi da yin magana daga maboyarsu.

Kara karanta wannan

An shiga jimami da 'yan bindiga suka kashe basarake mai daraja a Plateau

Buratai ya yi magana kan rashin tsaro
Tsohon shugaban rundunar sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya) Hoto: Tukur Buratai
Source: Facebook

Janar Tukur Buratai ya yi wannan jawabi ne a lokacin wata hira da ya yi da gidan talabijin na TVC ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2026.

Me Buratai ya ce kan gano 'yan bindiga?

A lokacin hirar, ya mayar da martani kan damuwar da ake da ita game da yadda ƙungiyoyin masu laifi ke ƙara amfani da dandalin sada zumunta da na'urorin ɗaukar bidiyo a faɗin ƙasar.

Tsohon Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin ya jaddada cewa hukumomi suna da cikakkiyar damar bin sawu da gano irin waɗannan masu aikata laifuffukan.

Buratai ya ce bai gaskata cewa hukumomin tsaro sun rasa ikon bin sawun 'yan bindigan da ke yawan tallata ayyukansu ba.

“Ba na jin sun kasa gano inda suke. Idan za su iya gano mutanen gari na ko masu yawan mabiya a dandalin sada zumunta, ba zan gaskata cewa za su kasa gano waɗannan 'yan bindigan da ke baje kolin ganimar da suka kwaso ko kuma duk wani aiki da suke yi ba."

Kara karanta wannan

Jagoran 'yan bindiga da suka sace tsohon janar a Katsina ya mika bukatunsa ga gwamnati

- Tukur Buratai

Buratai ya ba shawara kan tsaron Najeriya

Yayin da ya kauce wa sukar hukumomin tsaron kai-tsaye, Buratai ya yi hasashen cewa za a iya samun dalilai kan matakan gudanar da ayyukansu.

Tsohon shugaban rundunar sojojin kasan ya jaddada buƙatar ƙarfafa tsarin tsaron Najeriya ta hanyar gudanar da horo akai-akai, ɗaukar sababbin ma'aikata, da kuma inganta jin daɗin jami'an tsaro.

"Akwai buƙatar ƙarin jami'ai. Muna buƙatar ɗaukar ƙarin dakarun soji, ƙarin jami'an bincike, da kuma ƙarin 'yan sanda.”

- Tukur Buratai

Tukur Buratai ya ba da shawara kan tsaron Najeriya
Laftanar Janar Tukur Buratai (mai ritaya) a wajen wani taro Hoto: Tukur Buratai
Source: Facebook

'Yan bindiga sun hallaka basarake a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin da ya yi sanadiyyar rasuwar basarake a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya.

'Yan bindiga sun hallaka basaraken garin Timshat da ke karamar hukumar Langtang ta Kudu a jihar Plateau, Godwin Vonga, bayan sun tare shi a kan hanya.

Barasaken mai daraja wanda yake tsohon kansila ne ya gamu da ajalinsa ne, bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe shi a kan hanyar Timshat zuwa Mabudi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng