'Yan Bindiga Sun Sake Hallaka Mutane da Dama bayan Kashe Mutum 17 a Kauyen Sokoto

'Yan Bindiga Sun Sake Hallaka Mutane da Dama bayan Kashe Mutum 17 a Kauyen Sokoto

  • An sake shiga jimami a kauyen Dan Gulbi na jihar Sokoto sakamakon sabon harin da 'yan bindiga dauke da makamai suka kai
  • Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka mutane da dama tare da kona gidaje a sabon harin wanda suka kai a safiyar ranar Talata, 2 ga watan Yunin 2026
  • Sabon harin na zuwa ne sa'o'i 24 bayan da 'yan binddga suka hallaka mutane 17 ciki har da masu yawon sallah a kauyen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - 'Yan bindiga dauke da makamai sun sake kai hari a kauyen Dan Gulbi a karamar hukumar Tureta ta jihar Sokoto.

'Yan bindigan sun kai harin ne kwanaki biyu kacal bayan wani makamancin harin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17, ciki har da baƙin 'yan yawon Sallah.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Sokoto
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce mazauna yankin sun ce maharan, waɗanda suka zo da yawa a kan babura, sun farmaki kauyen ne da misalin ƙarfe 8:00 na safiyar ranar Talata, 2 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

"Za a iya gano su"; Buratai ya dauko batun 'yan bindigan da ke fitowa a bidiyoyi

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Sokoto

'Yan bindgan sun fara harbi ba kakkautawa, wanda hakan ya tilasta wa mazauna ƙauyen guduwa domin neman tsira.

Majiyoyi daga al'ummar ƙauyen sun yi zargin cewa aƙalla mutane 20 ne aka kashe a lokacin wannan sabon hari, yayin da aka ƙona gidaje da dama sannan wasu mutane da dama ba a gansu ba.

'Yan bindiga sun yi barna

Wani mazaunin yankin wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce maharan sun afka musu ne a daidai lokacin da mutane suka tattaru a ƙarƙashin inuwar rumfuna, kuma sun kwashe tsawon sa'o'i da dama a ƙauyen bayan sun kai harin.

“Sun zo ne suka fara harbe-harbe a kanmu. Mutane sun gudu ta kowane bangare domin ceton rayukansu,” in ji majiyar.

A ranar Lahadi, 'yan bindiga dake kan babura fiye da 150 suka kai hari a wannan kauyen, inda suka kashe mutane 17 tare da kwashe kayan shaguna kusan 20.

Kara karanta wannan

An shiga jimami da 'yan bindiga suka kashe basarake mai daraja a Plateau

Wannan lamari da ke ci gaba da faruwa ya tilasta wa mazauna yankin kiran hukumomin tsaro da sauran mahukunta abin ya shafa da su kawo masu agajin gaggawa.

'Yan bindiga sun yi ta'asa a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Yayin da aka tuntuɓe shi, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufai, ya ce rundunar ta samu kiran gaggawa na neman taimako daga Tureta, kuma nan take ta tura jami'anta zuwa yankin.

Kakakin 'yan sandan ya ƙara da cewa ana jiran cikakken rahoto daga jami'an da aka tura zuwa kauyen.

'Yan bindiga sun kashe basarake a Plateau

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun yi ajalin wani basarake a jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.

Tsagerun 'yan bindiga sun hallaka basaraken garin Timshat da ke karamar hukumar Langtang ta Kudu a jihar Plateau, Godwin Vonga.

Barasaken riga mu gidan gaskiya ne bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe shi a kan hanyar Timshat zuwa Mabudi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng