Kwankwaso Na Shirin Jagorantar Zanga Zanga kan Rashin Tsaro? An Ji Gaskiyar Magana
- An yada wata jita-jita mai nuna cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na shirin jagorantar zanga-zanga don nuna adawa da rashin tsaro
- Dan takarar mataimakin shugaban kasar a zaben 2027 ya fito ya yi magana kan alakanta shi da aka yi da batun zanga-zanga
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa ba ya goyon bayan duk wani abu wanda zai iya kai wa ga karya doka da oda
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi martani kan shirin jagorantar zanga-zanga.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya musanta cewa yana shirin jagorantar zanga-zanga domin nuna adawa da matsalar rashin tsaro.

Source: Facebook
Tsohon dan takarar shugaban kasar a zaben 2023 ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Litinin, 1 ga watan Yunin 2026.
An yada jita-jita kan Rabiu Kwankwaso
An dai yada wata jita-jita mai cewa Kwankwaso wanda ya mulki Kano har sau biyu yana shirin jagorantar zanga-zanga kan matsalar rashin tsaro.
A cewar jita-jitar dai, tuni Kwankwaso ya fara tattaro kan matasa domin ganin an gudanar da zangar-zangar da za ta nuna fushin halin da ake ciki.
Wane martani Kwankwaso ya yi?
Sai dai, a martanin da ya yi, Kwankwaso ya nuna cewa gaba daya babu kamshin gaskiya a cikin jita-jitar wadda aka yada.
Kwankwaso ya bayyana cewa bai goyon bayan abin da zai sanya a samu karyewar doka da oda a cikin kasar nan.
"Hankalinmu ya karkata ga wani saƙo da ke yawo a halin yanzu a dandalin sada zumunta wanda ke da'awar ƙarya cewa muna shirin gudanar da zanga-zanga kan ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar."
"Ba mu goyon bayan kowane irin mataki da zai iya kaiwa ga rugujewar doka da oda ko kuma lalata rayuka da dukiyoyi."
"A matsayinmu na shugabanni wadanda suka san ya kamata, muna ci gaba da kasancewa masu jajircewa ga hanyoyi na zaman lafiya da gina ƙasa wajen tunkarar ƙalubalen ƙasa."
"A matsayinmu na masu kishin dimokuraɗiyya da suka sadaukar da kai, mun yi amanna da gaske cewa akwatin zaɓe shi ne mafi halastacciyar hanya kuma mafi inganci ta bayyana ƙorafi da neman canji."
"Jam'iyyar mu, NDC, tana da yakinin samun gagarumar nasara a zaɓubbuka masu zuwa ta hanyoyin dimokuraɗiyya na zaman lafiya."
"Saboda haka, ana shawarartar babban taron jama'a da su yi watsi da wannan saƙo na ƙarya kuma su kauce wa waɗanda ke yaɗa irin wannan labari na karkatarwa."
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Source: Facebook
Ganduje ya yi wa Kwankwaso martani
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, martani.
Abdullahi Umar Ganduje ya yi ikirarin cewa a farkon siyasarsu, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yaron sa ne, akasin yadda shi yake nuna wa duniya.
Tsohon shugaban na jam'iyyar APC ya ce ya taimaka wa madugun na Kwankwasiyyar har ya tafi Majalisar dokoki ta kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

