Gwamna Abba Ya Yi Sauyi a Gwamnatin Kano, Ya Hade Wasu Ma'aikatu

Gwamna Abba Ya Yi Sauyi a Gwamnatin Kano, Ya Hade Wasu Ma'aikatu

  • Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusif ta dauki matakin hade wasu ma'aikatu guda biyu a wuri guda
  • An hade ma'aikatar albarkatun ruwa da ma'aikatar muhalli da canjin yanayi wuri guda ta yadda za su ci gaba da gudanar da ayyukansu
  • Matakin hadewar dai na zuwa ne bayan a kwanakin baya kwamishinan da ke kula da ma'aikatar ruwa ya yi murabus daga mukaminsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta hade wasu ma'aikatu wuri guda.

Gwamnatin ta Gwamna Abba ta sanar da haɗe ma'aikatar albarkatun ruwa da kuma ma'aikatar muhalli da canjin yanayi zuwa ma'aikata guda ɗaya tilo.

Gwamnatin Kano ta hade wasu ma'aikatu
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 1 ga watan Yuni, 2026, wadda sakataren gwamnatin jihar, Umar Farouk Ibrahim, ya sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai harin ta'addanci a Sokoto, an kashe masu yawon Sallah

An hade ma'aikatu biyu a Kano

A yanzu, sabuwar ma'aikatar za a riƙa kiran ta da ma'aikatar albarkatun ruwa, muhalli da canjin yanayi biyo bayan hadewar da aka yi.

Gwamnatin Abba ta bayyana cewa matakin yana da nufin haɓaka ingancin gudanarwa, inganta haɗin gwiwar manufofi, da kuma adana yadda ake amfani da albarkatu wajen tafiyar da al'amuran da suka shafi muhalli da ruwa a faɗin jihar.

A cewar takardar, sabuwar ma'aikatar za ta yi aiki ne ta hanyar manyan bangarori uda biyu; rukunin gudanarwa na albarkatun ruwa da kuma rukunin gudanarwa na muhalli da canjin yanayi, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

Wani bangare na cewa:

“Kowannensu zai kasance ƙarƙashin jagorancin babban sakatare inda duka biyun za su riƙa kai rahotonsu kai-tsaye ga mai girma kwamishina."

An sanar da bangarorin gwamnati

Ta kuma ƙara da cewa an umarci bangarori, hukumomi, da rukunoni da ke ƙarƙashin tsofaffin ma'aikatun da su daidaita ayyukansu da tsarin ba da rahotonsu cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.

Kara karanta wannan

Ma'aikatan gwamnatin tarayya sun yi watsi da tayin N100,000 a matsayin mafi karancin albashi

An aike da wannan umarni ga manyan jami'an gwamnati, ciki har da shugaban ma'aikatan fadar gwamnati, kwamishinoni, shugaban ma'aikatan gwamnati da kuma shugabannin hukumomin gwamnati, tare da kiran da a yaɗa saƙon sosai kuma a yi biyayya da shi daki-daki.

An hade wasu ma'aikatu a jihar Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jawabi Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Tsohon kwamishina ya yi murabus

Tun bayan murabus ɗin kwamishinan ruwa, Umar Haruna Doguwa, wanda daga baya ya zama shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, an ba abokin aikinsa na ma'aikatar muhalli, Dahir M. Hashim, ikon kula da ma'aikatar.

Kodayake takardar ba ta bayyana takaimaimai ba, amma ana hasashen cewa Dahir M. Hashim ne zai ci gaba da kasancewa mai kula da wannan sabuwar ma'aikata da aka haɗe.

Gwarzo ya soki gwamnatin Abba

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo, ya soki gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

Aminu Abdussalam Gwarzo ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da gazawa wajen sauke nauyin da ke kansa na kare rayuka da dukiyoyin mazauna jihar Kano.

Tsohon mataimakin gwamnan ya ba da hujjarsa cewa ƙalubalen tsaron jihar sun karu ne bayan da gwamnati ta ƙaddamar da tsarin nan nata na “Kano First”.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng