Manyan Labarai A Yau
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya ta nuna farin cikinta kan matakin da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya dauka na shigowa cikinta daga PDP.
Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Olabode George ya zargi Atiku Abubakar da Nyesom Wike da cin dunduniyar jam'iyyar. Ya bukaci su fice daga PDP.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a jihar Sokoto. Harin na 'yan bindigan ya kusa ritsawa da shugaban karamar hukumar Tangaza, Isa Kalanjeni.
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Dele Momodu, ya shawarci shugaban kasa Bola Tinubu da ka da ya yarda da 'yan siyasa masu sauya sheka zuwa APC.
Shugaban kasan Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya shiga ganawar sirri da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro da babban hafsan tsaro, Janar Christopher Musa.
Hadimin gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo ya bayyana cewa Sanata Neda Imasuen na jam'iyyar LP zai sauya sheka zuwa APC mai mulki a Najeriya.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da bindiga sun kai hare-hare a jihar Zamfara. 'Yan bindigan sun kashe jami'in tsaro tare da yin awon gaba da mutane masu yawa.
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya jajantawa mutanen Benue kan hare-haren 'yan bindiga. Ya ce gwamnatin tarayya za ta dauki mataki.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Kano, sun yi arangama da wani hatsabibin dan daba mai suna Baba Beru. 'Yan sandan sun aika da shi barzahu bayan fafatawa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari