Hadimin Gwamna Ya Fadi Sanatan LP da Zai Koma Jam'iyyar APC
- Mai ba gwamnan jihar Edo shawara kan harkokin siyasa, Eugene Utubor, ya ce sanatan LP zai koma jam'iyyar APC mai rinjaye
- Eugene Utubor ya bayyana cewa nan gaba kaɗan Sanata Neda Imasuen zai fice daga jam'iyyar LP mai hamayya zuwa APC
- Ya bayyana cewa sun gana da sanatan a ranar Talata kuma alamunsa sun nuna cewa ya shirya tattara kayayyakinsa daga jam'iyyar LP
- Neda Imasuen ya sha ƙin yin magana kan ci gaba da zamansa a LP wacce ke fama da rikicin cikin gida a matakin jiha da na ƙasa
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Mai ba gwamnan jihar Edo shawara na musamman kan harkokin siyasa, Eugene Utubor, ya bayyana cewa Sanata Neda Imasuen na jam’iyyar LP zai koma APC.
Hadimin na Gwamna Monday Okpebholo ya bayyana cewa nan gaba kaɗan Neda Imasuen zai koma jam’iyyar APC.

Asali: Twitter
Jaridar The Punch ta rahoto cewa Eugene Utubor ya gana da Sanata Neda Imasuen a daren Talata a birnin Benin, babban birnin jihar Edo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanatan jam'iyyar LP zai koma APC
Hadimin gwamnan ya bayyana cewa sanatan yana da niyyar sauya sheƙa zuwa APC, kuma an riga an fara ɗaukar matakai domin tabbatar da cewa ya ƙarfafa jam’iyyar a matakin ƙasa da na jiha.
Jam’iyyar LP dai a jihar da kuma a matakin ƙasa na fama da rikicin shugabanci da kuma rabuwar kawuna.
Sanata Neda Imasuen wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan ɗa'a ya sha gujewa tambayoyi da suka shafi ci gaba da kasancewarsa a LP, saboda rikicin da ya addabi jam'iyyar.
"Ina tabbatar muku da cewa Sanata Neda Imasuen zai sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC nan ba da jimawa ba."
"Na kasance tare da shi a ranar Talata, kuma halayensa sun nuna hakan a fili."
"Neda Imasuen yana ganin cewa gwamna ya yi kyakkyawan aiki cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, kuma yana da matuƙar muhimmanci mu haɗa kai domin tallafa wa hangen nesan gwamnan domin ci gaban al’ummarmu.”
"Ya karfafa gwiwar kowane ɗan Edo mai kishin ci gaba da ya tsaya tsayin daka tare da gwamna a wannan aiki na gina jiha."
- Eugene Utubor

Asali: Twitter
Sanata Neda Imasuen na ɗasawa da shugabannin APC
A ƴan kwanakin nan, an sha ganin Sanata Imasuen a wuraren taruka da dama tare da fitattun shugabannin jam’iyyar APC a jihar Edo.
An ce yana da kyakkyawar alaƙa da mambobin jam’iyyar mai mulki a cikin jihar.
Gwamnan Delta ya koma jam'iyyar APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya fice daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.
Gwamna Oborevwori ya koma jam'iyyar APC bayan kammala wani taron sirri a fadar gidan gwamnatin jihar Edo.
Komawarsa jam'iyyar APC ta kawo ƙarshen raɗe-raɗin da ake yi kan cewa zai fice daga PDP wacce ya lashe zaɓen gwamnan 2023 a ƙarƙashinta.
Gwamna Sheriff Oborevwori ya samu tarba daga wajen shugabannin jam'iyyar APC a jihar Edo.
Asali: Legit.ng