Ana Jimamin Mutuwar Fafaroma, 'Yan Bindiga Sun Sace Malamin Addini a Kaduna
- Wasu miyagun ƴan bindiga sun bi dare sun yi awon gaba da wani limamin cocin Katolika a jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya
- Ƴan bindigan sun sace Rev. Fr. Ibrahim Amos ne bayan sun kutsa gidansa da ke Kurmin Risga a ƙaramar hukumar Kajuru
- An buƙaci jama'a su ci gaba da addu'o'i domin a gaggauta sako limamin na Katolika cikin ƙoshin lafiya daga hannun ƴan bindiga
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kaduna - A wani babban lamari mai tayar da hankali, ƴan bindiga sun sace wani limamin Katolika, Rev. Fr. Ibrahim Amos, a jihar Kaduna.
Ƴan bindigan sun sace malamin addinin ne a garin Kurmin Risga, da ke cikin ƙaramar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.

Asali: Twitter
Rahoton jaridar The Punch ya bayyana cewa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12:15 na daren ranar Laraba, 23 ga watan Afirilun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda ƴan bindiga suka sace malamin addini
Ƴan bindigan da suka aikata wannan mummunan aiki sun kutsa kai cikin gidan limamin da ke St. Gerald Quasi Parish a Kurmin Risga, inda suka yi awon gaba da shi.
Shugaban cocin Catholic Diocese na Kafanchan, Rev. Fr. Jacob Shanet, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis.
A cikin sanarwar, ya bayyana cewa wannan lamari ya girgiza su matuƙa kuma ya kasance abin baƙin ciki da damuwa ga dukkan mabiya cocin da al’ummar garin.
"Muna buƙatar addu'o’inku don Amallah Ya sa a sako limaminmu cikin gaggawa da ƙoshin lafiya."
"Muna bukatar jama’a su kwantar da hankalinsu, su kau da kai daga ɗaukar doka a hannunsu, domin za mu yi amfani da duk wata hanya ta doka ta tanada domin ganin an kuɓutar da limamin cikin koshin lafiya kuma ba tare da wata illa ba."
- Rev Fr. Jacob Shanet
Ƴan sanda ba su san da harin ba
Legit Hausa ta tuntuɓi jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, domin samun ƙarin bayani a kan lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa bai da masaniya kan harin amma zai bincika ya gani.
"Yanzu ina tafiya ne, idan na sauka zan bincika na gani."
- DSP Mansur Hassan

Asali: Original
Wannan lamari ya sake jaddada matsalar tsaro da ke addabar wasu sassan Arewacin Najeriya, musamman satar mutane domin karbar kudin fansa.
Ana fatan hukumomi za su ƙara ƙaimi wajen tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin jama’a, tare da gaggauta daukar matakin ceto Rev. Fr. Ibrahim Amos cikin aminci.
Ƴan bindiga sun kai hare-hare a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu ƴan binɗiga sun kai hare-hare a ƙananan hukumomi guda uku na jihar Zamfara.
A yayin hare-haren, ƴan bindigan sun kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba tare da yin awon gaba da wasu da dama.
Tantiran ƴan bindigan sun kuma hallaka wani jami'in tsaro na rundunar Askarawan Zamfara bayan sun tare motar da yake ciki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng