An Kama Makudan Kudaden Kasashen Waje a Kano, EFCC ta shiga bincike

An Kama Makudan Kudaden Kasashen Waje a Kano, EFCC ta shiga bincike

  • Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta fara binciken wani fasinja Haruna Yusuf kan wasu kudaden kasashen waje da aka kama a filin jirgin saman Kano
  • Jami’an Kwastam sun kwace kudin kasashe da suka hada da $73,000, £15,957 da 827,800 na Saudiyya da ake zargin ba a bayyana jami'ai su ba
  • EFCC da ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya ta ce rashin bayyana makudan kudaden ya saba wa dokar hana safarar kudade ta shekarar 2022

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kasa (EFCC) ta ce ta fara binciken wani mutum mai suna Haruna Yusuf.

An fara bnciken ne bayan an kama wasu makudan kudaden kasashen waje da ake zargin ba a bayyana su ba a filin jirgin saman Mallam Aminu Kano da ke Kano.

Kara karanta wannan

Tsaro: An gano biliyoyin Naira da jihohi 31 suka kashe a watanni 6 kacal

EFCC ta fara wani bincike a jihar Kano
Ofishin hukumar yaki da rashawa ta EFCC Hoto: Econocmic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

The Cable ta wallafa cewa wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Litinin, 17 ga watan Agusta, 2026.

An kama kudi a Kano

A ruwayar The Guardian, EFCC ta ce kudaden sun hada da $73,000, £15,957 da Riyal 827,800 na Saudiyya. An kama kudaden ne yayin binciken fasinjojin da ke shigowa Najeriya tsakanin ranar 8 zuwa 12 ga Agusta, 2026.

Mukaddashin shugaban hukumar kwastam na shiyyar Kano/Jigawa, U U Adamu, ya ce a ranar 8 ga Agusta, 2026 jami’an hukumar sun gano wata jaka ta Saudi Air ba ta tare da mai ita ba.

A lokacin, an gano cewa an boye jakar ne a cikin takalmi dauke da Riyal 827,800 da kuma $53,300 wanda hakan ya ja hankalin jami'ai.

Bayan kwanaki hudu, jami’an kwastam sun sake gano wata jaka mallakin Yusuf, wanda ya shigo Najeriya da jirgin Ethiopian Airlines mai lamba ET941.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sauya taku, an tura zazzafan gargadi ga 'yan ta'adda

Ana bincike kan kudin waje a Kano

Adamu ya ce binciken na biyu da aka gudanar ta hanyar amfani da fasahar zamani ta gano $20,000 da £15,957 da aka boye a cikin takalman motsa jiki.

EFCC ta ce an kama jami'an kwastam ne suka yi kamen kudi a filin jirgin Kano
Taswirar jihar Kano inda aka yi kame a filin jirgin Aminu Kano Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daga bisani, UU Adamu ya mika Yusuf da kudaden da aka kwato ga EFCC a madadin hukumar kwastam ta Najeriya. Sai dai sanarwar ba ta bayyana karara ko Yusuf ne mamallakin kudin Riyal 827,800 da aka gano ba.

UU Adamu ya ce kama kudaden ya nuna irin kokarin da jami’an Kwastam ke yi wajen dakile safarar kudaden kasashen waje da ba a bayyana ba ta kan iyakokin Najeriya.

Ya kara da cewa hukumar za ta ci gaba da karfafa hadin gwiwa da EFCC da sauran hukumomin tsaro domin yaki da laifukan kudi.

EFCC ta kai wani kotu

A baya, mun samu labarin cewa hukumar EFCC ta gurfanar da wani mutum a gaban babbar kotu bisa zargin damfarar Naira miliyan 56.5 da aka tara domin gudanar da aikin Hajjin 2023.

Kara karanta wannan

Yadda motoci suka nutse, komai ya tsaya cak bayan ambaliya a Abuja

Ana zargin ya karɓi kuɗin daga Ibrahim Shuaibu, bayan ya yi ikirarin cewa ma’aikacin gwamnatin Kaduna ne da zai taimaka wajen tabbatar da an shirya aikin hajji lafiya sumul.

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta ce mutane 10 da ake kiwon shanu a Oke-Ogun sun ba da kuɗin, amma babu wanda ya je Saudiyya saboda Musa bai cika alkawarinsa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng