Jigo a PDP Ya ba Tinubu Shawara bayan Sauya Shekar Gwamna zuwa APC

Jigo a PDP Ya ba Tinubu Shawara bayan Sauya Shekar Gwamna zuwa APC

  • Dele Momodu ya yi magana kan sauya sheƙar da gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori ya yi daga jam'iyyar PDP zuwa APC
  • Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasan na PDP ya shawarci Bola Tinubu da ka da ya mayar da Najeriya dimokuraɗiyyar kama-karya
  • Ya buƙaci shugaban ƙasan da ka da ya yarda da ƴan siyasan da ke tururuwa suna sauya sheƙa daga jam'iyyunsu zuwa APC mai-ci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP, Dele Momodu, ya ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu shawara.

Dele Momodu ya shawarci shugaban ƙasan da ka da ya maida Najeriya ƙasa mai mulkin kama-karya.

Dele Momodu ya ba Tinubu shawara
Dele Momodu ya ba Shugaba Bola Tinubu shawara kan 'yan siyasa Hoto: Dele Momodu
Asali: Facebook

Dele Momodu ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na tashar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi wannan magana ne a lokacin da yake sharhi kan ficewar gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, mataimakinsa Monday Onyeme, da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Wace shawara jigon PDP ya ba Tinubu?

Ya buƙaci shugaban ƙasan da ya mutunta tsarin dimokuraɗiyya, don ka da a koma ana yin kama-karya a Najeriya.

"Shawarata gare shi (Tinubu) mai sauƙi ce, ka mutunta ginshiƙan dimokuraɗiyya. Ka da ka mayar da Najeriya dimokuraɗiyyar kama-karya."
"Ko mene ne ya faru, kai mutum ne mai goyon bayan dimokuraɗiyya kafin ka zama shugaban ƙasa.”
"Don Allah ka ba dimokuraɗiyya dama ta numfasa a Najeriya. Idan ba haka ba, zan iya rantsewa da raina cewa wata rana hakan zai zama abin dana-sani ƙwarai."

- Dele Momodu

Dele Momodu bai yi mamakin ficewar Okowa PDP ba

Dele Momodu ya ce bai yi mamakin ficewar Ifeanyi Okowa zuwa jam’iyyar APC ba, yana mai cewa an daɗe ana matsa masa lamba da tsangwama.

Dele Momodu
Dele Momodu ya ce bai yi mamakin sauya sbekar gwamnan Delta zuwa APC ba Hoto: Dele Momodu
Asali: Facebook
"Ban yi mamaki ba game da hakan. Tsohon gwamnan yana fama da matsin lamba sosai a ƴan kwanakin nan; ba sabon abu ba ne."
"Abin da zai ba ni mamaki shi ne idan Shugaba Bola Tinubu yana ɗauka cewa mutane suna shiga APC ne saboda suna ƙaunarsa ko kuma saboda yana tafiyar da mulki cikin ƙwarewa.”
“Shawarata ga Asiwaju ita ce ka da ya yarda da waɗannan ƴan siyasa. A yanzu kowa na ganin cewa yana da niyyar neman wa’adi na biyu.”
“Allah ne ya ba shi wa’adi na farko, ba ta hanyar tursasawa ba. Ban san dalilin da yasa yanzu yake tunanin dole sai ya samu wa’adi na biyu ta hanyar tursasawa ba."

- Dele Momodu

Matsayin adawar PDP a siyasar Najeriya

A cikin shekaru baya-bayan nan, jam’iyyar PDP ta ci gaba da nuna rauni a matsayin babbar jam’iyyar adawa a Najeriya.

Bayan faduwar ta daga mulki a 2015, PDP ta kasa tsayawa da kafafunta wajen gina sabuwar manufa ko shugabanci mai karfi da zai jawo hankalin jama’a.

Yawan sauya sheƙa na manyan ‘yan siyasa daga PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki ya nuna irin gibin da ke cikin tsarin jam’iyyar – rashin daidaito, shugabanci maras karfi, da karancin tsari mai dorewa.

Ficewar sabbin jagorori kamar gwamnan Delta Sheriff Oborevwori da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa daga PDP zuwa APC na kara jaddada wannan raunana.

Jam’iyyar ba ta da ikon tsare manyan mambobinta, kuma hakan na rage mata karfi a matsayin adawa mai tasiri.

A lokaci da Najeriya ke bukatar adawa mai karfi don sa ido kan gwamnatin Tinubu, PDP na ci gaba da karyewa daga ciki.

Wannan ya bar fagen siyasa a hannun jam’iyya daya, lamarin da ke barazana ga dimokuraɗiyya.

A irin wannan yanayi ne Dele Momodu ke jan hankali, yana kira ga shugabannin APC su guji amfani da karfin iko wajen tursasa ‘yan adawa, domin hakan zai kai Najeriya ga tsarin kama-karya.

Shugaba Tinubu ya gana da Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya labule da dakataccen gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara.

Shugaba Tinubu ya gana da Gwamna Simi Fubara ne a birnin Landan kafin ya dawo gida Najeriya daga hutun da ya je yi.

A yayin ganawar ta su, sun tattauna batutuwa masu muhimmanci kan makomar siyasar jihar mai arziƙin mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng