"Jama'a Sun Waye": Jigo a APC Ya Hango Abin da Zai Sanya Tinubu Ya Fadi a 2027
- Jonathan Vatsa ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya salon mulkinsa tare da komawa wajen talakawa domin samun nasara a zaben 2027
- Tsohon kwamishinan na jihar Neja ya ce sakamakon zaben gwamnan Osun ya kamata ya zama babban gargadi ga jam’iyyar APC
- Vatsa ya ce yunwa, rashin aikin yi da matsin tattalin arziki na iya shafar damar Tinubu idan bai sake alakarsa da ’yan Najeriya ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Neja, Hon. Jonathan Vatsa, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauya salon mulkinsa tare da gaggauta komawa wajen ’yan Najeriya idan yana son samun nasara a zaben shugaban kasa na 2027.
Vatsa, wanda ya taba zama kwamishinan yada labarai, al’adu da yawon bude ido na jihar Neja, ya ce sakamakon zaben gwamnan jihar Osun na baya-bayan nan babban gargadi ne ga APC.

Source: Twitter
Tashar Channels tv ta kawo rahoton cewa ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a Minna, babban birnin jihar Neja.
Ya ce sakamakon zaben ya nuna cewa dogaro da tsarin siyasa da gwamnoni kadai ba zai wadatar wajen tabbatar wa Shugaba Tinubu nasara a 2027 ba.
Vatsa ya ce yadda APC ta gudanar da harkokinta a zaben Osun ya nuna bukatar jam’iyyar ta koma kan turbar tuntubar talakawa tare da magance matsalolin tattalin arzikin da ke addabar ’yan Najeriya.
Vatsa ya gargadi APC
Vatsa ya ce yawan gwamnonin APC da suka taru a Osun amma suka dawo ba tare da nasara ba alama ce da ke nuna cewa jam’iyyar ta rasa amincewar jama’a.
A cewarsa, Shugaban na iya yin kuskure wajen barin gwamnonin jihohi su mallaki kudaden da aka samu sakamakon cire tallafin man fetur.
Sai dai ya ce har yanzu lokaci bai kure ba, domin gwamnati za ta iya sauya salon tafiyar da harkokinta tare da sake kulla alaka kai tsaye da talakawa.

Kara karanta wannan
Bayan shan kashi a Osun, shugaban matasan APC ya ba jam'iyyar mafita kan zaben 2027
Vatsa ya ce yadda mutanen Osun suka kada kuri’a ya bayyana halin da ’yan Najeriya ke ciki.
“Dole ne in ce mutanen jihar Osun sun bayyana abin da ’yan Najeriya ke ji ta yadda suka kada kuri’a a zaben. ’Yan Najeriya ba sa farin ciki saboda wahalhalun rayuwa duk da yawan kudaden da ke cikin kasa.” In ji shi.
Zaben Osun ya zama gargadi
Vatsa ya yi zargin cewa ana karkatar da kudaden da aka samu daga cire tallafin man fetur zuwa ga gwamnatocin jihohi ba tare da samun ingantaccen sauyi a rayuwar jama’a ba.
Ya ce hakan ya sa ’yan Najeriya ke kallon Shugaban kasa a matsayin wanda ke da alhakin matsin tattalin arzikin da suke fuskanta.
“Daga yadda mutanen Osun suka kada kuri’a tare da kare kuri’unsu, wannan alama ce cewa ’yan Najeriya sun shirya kada kuri’a tare da kare kuri’unsu a 2027."
“Wannan gargadi ne karara kan abin da APC ya kamata ta sa ran gani a 2027, domin gwamnonin suna yada talauci a jihohinsu,” in ji shi.
Wace shawara ya ba Shugaba Tinubu?
Ya bukaci Shugaba Tinubu ya koma kan turba ta tuntubar talakawa tare da sake kulla alaka da ’yan Najeriya idan yana son samun wa’adin mulki na biyu.
“Jama’a sun fi wayewa yanzu; da gaske suke yi kan abin da suke so, sun kuduri aniyar bijirewa tsoratarwa kuma sun shirya kada kuri’a bisa abin da zuciyarsu ta gaya musu. Ya kamata Shugaban kasa ya lura da wannan sauyin,” in ji Vatsa.

Source: Twitter
Tinubu ya yabawa Janar IBB
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), murnar cika shekaru 85 da haihuwa.
Mai girma Tinubu ya bayyana tsohon shugaban a matsayin wanda ya yi wa Najeriya ayyuka masu tasiri ta hanyoyin da babu wani shugaban kasa da ya taɓa yi.
Asali: Legit.ng

