Yadda Dalibin Tsangaya Ya Tsallake Rijiya da Baya Lokacin da Abokansa 4 Suka Rasu a Kano
- Daliban tsangaya huɗu sun mutu a Kano bayan sun kamu da rashin lafiya sakamakon cin wani kifin da ake zargin yana dauke da guba
- Ɗalibi na biyar ya tsira bayan ya ƙi ci gaba da cin kifin saboda ya lura ɗanɗanonsa ya canja kuma akwai sauran kwanakinsa a gaba
- An kai waɗanda lamarin ya rutsa da su asibitoci daban-daban kafin a tabbatar da mutuwar daliban a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Daliban tsangaya huɗu sun rasa rayukansu a Jihar Kano bayan sun kamu da rashin lafiya sakamakon cin wani kifin da ake zargin ya gurɓace, yayin da wani ɗalibi na biyar ke karɓar magani a asibiti.
Yaran da suka rasu sun hada da Abdulfatah Mohammed mai shekaru 15, Yusuf Nuhu mai shekaru 16, Buhari Iliyasu mai shekaru 14 da Ibrahim Muhammad mai shekaru 22.

Kara karanta wannan
Dalibai 4 na makarantar haddar Kur'ani sun mutu lokaci guda a jihar Kano, an gano dalili

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta kawo labarin cewa kungiyar Tsangaya Media Networa tabbatar da rasuwar daliban tare da bayyana halin da ake ciki bayan afkuwar lamarin.
Yadda dalibi ya tsira a Kano
Rohoton Daily Trust ya bayyana cewa dalibi na biyar, Auwalu Surajo mai shekaru 18, ya tsira bayan ya ƙi ci gaba da cin kifin, kuma a halin yanzu yana karɓar magani.
Daliban suna karatu ne a makarantar Tsangaya mallakin Gwani Malam Iliyasu Mai Tsangaya da ke Kadage Sharifai, Ƙaramar Hukumar Ungogo a Kano.

Source: Original
Surajo Unguwar Gareji, wani abokin ɗaya daga cikin marigayin, ya shaidacewa lamarin ya faru ne bayan wani daga cikin ɗaliban ya fito da kifin da misalin ƙarfe 7 na safe, inda suka fara ci.
Ya ce shi ma ya ɗanɗana kifin, amma ya daina ci nan take bayan ya lura cewa ɗanɗanonsa ba irin na yau da kullum ba ne.
“Na ɗanɗana kifin, amma nan take na daina ci saboda ɗanɗanonsa bai yi daidai ba."
Yadda daliban Kano suka rasu
A cewarsa, jim kaɗan bayan sauran ɗaliban sun ci kifin, huɗu daga cikinsu suka kama rashin lafiya. Ya ce an sanar da malaminsu lamarin, wanda nan take ya shirya aka kai waɗanda abin ya shafa asibiti.
Gwani Sani Musa Nuhu wanda shi ne shuganam kungiyar tsangaya a yankin, ya bayyana tun da farko cewa an garzaya da ɗaliban zuwa Asibitin Koyarwa na Aminu Kano.
A cikin wata sanarwa, ya ce ɗaliban huɗu sun mutu a asibitin a daren Lahadi, 16 ga Agusta kuma a yanzu haka an riga an yi masu sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
Gini ya fadowa dalibai
A wani labarin, mun wallafa cewa mutane biyar, ciki har da ma’aikatan gini huɗu da wata daliba ta makarantar Islamiyya lamarin da ya jefa jama'a a cikin rashin sukuni.
Hatsarin farko ya faru ne a Gaida, kusa da gidan mai na Salbas, inda wani ginin da ake ginawa wanda bai kammala ba ya ruguje kan ma’aikata shida, mutun hudu daga ciki suka rasu.
Lmari na biyu ya faru ne bayan kusan mintuna shida a Kurna, a bayan makarantar firamare, inda wani ginin makarantar Islamiyya mai suna Khadija Idris Bala ya ruguje har daliba daya ta rasu.
Asali: Legit.ng
