"Yadda El Rufai Zai Iya Kawo karshen Mulkin Tinubu a 2027", Masanin Siyasa

"Yadda El Rufai Zai Iya Kawo karshen Mulkin Tinubu a 2027", Masanin Siyasa

  • Masana kan harkokin siyasa na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027
  • Majeed Dahiru ya bayyana cewa Nasir El-Rufai zai iya kawo ƙarshen mulkin Bola Tinubu, ya hana shi zarcewa a ofis
  • Ya nuna hakan zai yiwu ne idan tsohon gwamnan na Kaduna ya sanya ƴan Arewa suka goyi bayan Peter Obi na jam'iyyar LP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Masanin siyasa kuma mai sharhi kan harkokin jama’a, Majeed Dahiru, ya yi magana kan yadda za a iya kawo ƙarshen mulkin Shugaba Bola Tinubu a 2027.

Majeed Dahiru ya bayyana cewa mulkin Shugaba Tinubu zai iya ƙarewa a 2027 idan Nasir El-Rufai, ya samu nasarar haɗa kan manyan ƴan siyasar Arewa su marawa Peter Obi na jam’iyyar LP baya.

Nasir El-Rufai da Bola Tinubu
Majeed Dahiru ya ba EL-Rufai shawara kan zaben 2027 Hoto: @elrufai, @DOlusegun
Asali: Twitter

Majeed Dahiru ya bayyana hakan ne a wani shirin The Morning Brief na Channels Tv a ranar Juma’a, 25 ga watan Afirilun 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masanin ya yi tsokaci kan tattaunawar da ke gudana game da haɗakar jam’iyyun adawa da kuma rawar da El-Rufai ke takawa a ƙulle-ƙullen siyasa gabanin babban zaɓen da ke tafe.

Batun rigimar El-Rufai da Tinubu

Da yake magana kan ficewar El-Rufai daga jam’iyyar APC zuwa SDP, Majeed Dahiru ya bayyana saɓanin da ke tsakaninsa da Tinubu a matsayin wanda ya shafi bambancin ra’ayi da kuma na ƙashin kai.

“El-Rufai yana da ƙorafi kan shugaban ƙasa, ƙorafi ne na gaskiya domin ya taimaka masa sosai wajen samun mulki. Ko kana sonsa ko kana ƙinshi, yana da hujjar yin fushi."
"Yana aiki tuƙuru domin ganin ya karya tasirin shugaban ƙasa, musamman a wajen Musulman Arewa, inda yake kamar Khalifan Buhari. Shi ne ƙwaƙwalwar siyasar Musulman Arewa."

- Majeed Dahiru

Yadda El-Rufai zai kawo ƙarshen mulkin Tinubu

Majeed Dahiru ya ƙara da cewa El-Rufai na iya canza akalar siyasar Najeriya gaba ɗaya idan har ya yanke shawarar marawa ɗan takara daga Kudu baya, musamman daga Kudu maso Gabas.

Nasir El-Rufai
El-Rufai na cikin masu hadaka don kawar da Tinubu a 2027 Hoto: @elrufai
Asali: Twitter
“Bari na ba shi shawara, idan har yana son kawowa shugaban ƙasa cikas, abin da ya kamata ya yi, kuma ina ganin wataƙila suna kan wannan hanya, shi ne ya shawo kan Musulman Arewa su duba Kudu domin neman ɗan takara. Musamman Kudu maso Gabas."
“Idan ya iya yin hakan, kuma na san yana da ƙarfin yin hakan, zai iya karkatar da goyon baya zuwa ga mutum kamar Peter Obi, to hakan zai zama ƙarshen mulkin Shugaba Tinubu."
“Ina so na fadi a fili, ranar da El-Rufai ya yanke shawara kuma ya samu damar hada kan masu ruwa da tsaki a Arewacin Najeriya domin goyon bayan Peter Obi a matsayin ɗan takara, to wannan rana ce ƙarshen mulkin Tinubu."

- Majeed Dahiru

Jigo a SDP ya ja kunnen El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar SDP a 2023, Adewole Adebayo, ya gargaɗi Nasir El-Rufai.

Adebayo ya bayyana cewa ba za su yarda ƴan adawa su ƙwace SDP ba domin yaƙar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Babban ƙusan na SDP ya bayyana cewa ba za su amince a kawo musu faɗan da babu ruwansu da shi ba a jam'iyyar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng