2027: Jigo a PDP Ya Taso Wike da Atiku a Gaba, Ya Fadi Hukuncin da Ya Dace da Su
- Tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Olabode Geroge ya yi kalamai masu kaushi kan Atiku Abubakar da Nyesom Wike
- Olabode George ya buƙaci manyan ƴan siyasan da su fice daga jam'iyyar PDP mai hamayya saboda zargin yi mata zagon ƙasa
- Ya bayyana cewa ba zai tsaya ya zura ido yana kallo ba Atiku da Wike su ci gaba da kunyata PDP da ta shafe sfhekaru 16 a mulki ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Olabode George, ya ce dole ne Atiku Abubakar da Nyesom Wike, su gaggauta ficewa daga PDP.
Olabode George ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasan da ministan birnin tarayya Abuja, su fice daga PDP ne saboda zargin cin dunduniyarta.

Asali: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba a Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa manyan ƴan siyasan biyu suna kunyata jam'iyyar PDP kan yadda suke alaƙa da APC a bayyane, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Tsohon shugaban PDP ya caccaki Atiku, Wike
Ya zargi Atiku da Wike da yin cudanya da ƴan adawa, yana mai cewa ba za su iya ci gaba da iƙirarin kasancewa ƴan jam’iyyar adawa mafi girma ba, duba da iri abubuwan da suke yi.
“Me ke faruwa ne? Duk wanda ya gaji da PDP ya kamata ya fice ya shiga wata jam’iyya. Wannan abin kunyan ya isa haka."
“A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda kafa wannan jam’iyya, ba zan zauna ina kallo wasu na nuna rashin girmamawa ga jam’iyyar a fili ba. Wannan abu ne da ba zai yuwu ba."
- Olabode George
Olabode George ya yi tambaya kan dalilin da ya sa Atiku, tare da wasu, suka kai ziyara ga tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Kaduna.
Haka kuma, jigon na PDP ya soki abin da ya kira goyon baya da wasu gwamnoni da shugabannin PDP ke bai wa Shugaba Bola Tinubu a fili kafin zaɓen 2027.
Wane mataki ya kamata a ɗauka kan Wike, Atiku?

Asali: Twitter
“Yanzu ne lokacin da shugabannin PDP na ƙasa ya kamata su ɗauki mataki mai ƙarfi don ceto jam’iyyarmu mai girma."
"A matsayina na ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar kuma dattijo, ina kira ga sauran dattawan jam’iyyar su dakatar da Atiku da Wike, domin ba su fi jam’iyyar girma ba."
"Batun Wike kuwa a bayyane yake. Yana ƙoƙarin ci gaba da kasancewa da Tinubu yana kuma aiki da jam’iyyar adawa."
"Ba ƙaramin yaro ba ne kuma yana san abin da ya dace da shi a siyasa, amma ba zai yiwu kace kai ɗan PDP ne kuma kana aiki da abokan gaba ba."
“Yana shirya hira kai tsaye a tashoshin talabijin tamkar shi ne shugaban ƙasa yana cin mutuncin PDP a cikin hirar. Idan har yanzu akwai ragowar kunya a tattare da shi, to yanzu ne lokacin da ya kamata ya fice daga jam’iyyarmu."
- Olabode George
Jigon PDP ya caccaki gwamnonin jam'iyyar
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban ƙusa a jam'iyyar PDP, Olabode George, ya nuna takaicinsa kan shirin wasu gwamnonin PDP na komawa APC
Jigon na PDP ya bayyana yunƙurin gwamnonin a matsayin babban cin amana duba da irin damar da PDP ta ba su na hawa kan madafun iko.
Tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa ya ƙara da cewa abin kunya ne gwamnonin su watsawa jam'iyyar da ta tallafa musu ƙasa a ido.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng