Amarya da Ango Sun Mutu a Mummunan Hatsarin Jirgin Sama yayin Cin Amarci
- Wasu sababbin ma’auratan Birtaniya, Alexander Cromie da Marie Ebert, sun mutu tare da matukin jirgi bayan wani mummunan hatsari
- Ma’auratan sun je Girka ne domin bikin amarcinsu, inda suka yi amfani da jirgin sama mai saukar ungulu daga Markopoulo kusa da Athens zuwa tsibirin
- Hukumomin tsaron jiragen sama na Girka sun fara bincike kan hatsarin, yayin da jami’an ceto suka kashe gobarar da ta tashi bayan hatsarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
London, UK - Wani matashi ɗan Birtaniya da amaryarsa sun mutu tare da matukin jirginsu bayan wani jirgin sama mai saukar ungulu.
An bayyana sunayen ma’auratan da Alexander Cromie da Marie Ebert, waɗanda suka je Girka domin bikin amarcinsu cikin farin ciki.

Source: Getty Images
An yi hatsarin jirgin sama a Girka
Jirgin mai zaman kansa ya yi hatsarin ne kusa da wurin saukar jiragen, inda ma’auratan da matukin jirgin, ɗan ƙasar Girka, suka mutu, cewar BBC.
Rahotanni sun ce ma’auratan sun tashi da jirgin daga ƙauyen Markopoulo kusa da Athens zuwa shahararren tsibirin yawon buɗe ido na Sifnos.
Hukumar kula da tsaron jiragen sama ta Girka ta shaida cewa ta fara bincike kan hatsarin da ya faru ranar Litinin.
Masu binciken hukumar za su isa wurin ranar Talata domin tattara hujjoji tare da tattaunawa da mutanen da suka ga abin da ya faru.
Majiyoyi sun ce an tuntubi Ma’aikatar Harkokin Wajen Birtaniya, hukumomin Girka da kamfanin jirgin domin jin ƙarin bayani kan hatsarin.
Kamfanin Blackstone, inda Cromie ke aiki, ya bayyana cewa ya girgiza matuƙa da rasuwar mutane uku, ciki har da abokin aikinsu Alex Cromie da matarsa Marie Ebert.
Ya ce Alex mutum ne da kowa ke ƙauna a tsakanin mutanen da suka san shi kuma suka yi aiki tare da shi a Blackstone, cewar Sky News.

Source: UGC
Yadda aka gano jirgin na faduwa

Kara karanta wannan
Mutane sun mutu da gine gine 2 suka rufta kan ɗaliban Islamiyya da ma'aikata a Kano
Jami’an agajin gaggawa da mazauna yankin sun isa wurin hatsarin, inda suka yi ƙoƙarin kashe gobarar da ta tashi bayan jirgin saman ya faɗi.
Mataimakin magajin garin Sifnos, Manolis Foundoulakis, ya isa wurin jim kaɗan bayan hatsarin, inda ya ce kusan babu wani abu da ya rage daga jirgin.
Ya ce mazauna yankin sun ga jirgin yana faɗuwa ne a tsakanin ‘yan mitoci da gidajensu yayin da yake shirin sauka.
Foundoulakis ya ce mutanen yankin sun ji wani sautin injin da ya bayyana musu a matsayin abin mamaki yayin da jirgin ke gab da sauka.
Ya ce an gano gawarwakin mutane biyu a cikin tarkacen jirgin, yayin da aka samu mutum na uku a ɗan nesa da wurin hatsarin.
‘Yan kwana-kwana sun yi ƙoƙarin shawo kan gobarar da ta tashi bayan hatsarin, kuma an samu nasarar kashe ta zuwa yammacin ranar Litinin.
Amarya ta kashe angonta da guba
Mun ba ku labarin cewa rundunar ‘yan sandan Bauchi ta kama wata matar aure mai shekaru 19 bisa zargin yunƙurin kashe mijinta ta hanyar sanya masa guba a abinci.

Kara karanta wannan
Abin tausayi: Hatsarin jirgi ya rutsa da manoma a hanyar zuwa gonakinsu a Najeriya
An ce matar, Aisha Musa, wadda ta yi aure kimanin kwanaki 40 da suka wuce, ta sanya wani abu da ake zargin guba ne a cikin abincin mijinta.
Yan sanda sun ce sun kama matar bayan samun rahoton lamarin, yayin da aka garzaya da mijin asibiti inda yake samun kulawa kuma halin da yake ciki ya daidaita.
Asali: Legit.ng
