'Ya Fi na Najeriya': An Ji Albashin da Shugaban Kasar Amurka Yake Dauka a Shekara
- Shugaban ƙasar Amurka na karɓar albashi na $400,000 a shekara, kuma an ce albashin yana fitowa ne daga harajin 'yan ƙasa
- An ce Shugaba Donald Trump bai karɓi albashi ba a mulkinsa na farko, yana raba kudin ga ma’aikatu don tallafa wa aikin gwamnati
- Bayan sauka daga mulki, shugaban ƙasar Amurka zai ci gaba da samun $244,000 a shekara, da tsaro, lafiya da tafiye-tafiye na gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Amurka - A ganinka, nawa ne shugaban ƙasar Amurka ke karɓa a shekara a matsayin albashi?
Wataƙila ka ɗauka cewa saboda yana matsayin lamba ɗaya a Amurka kuma ɗaya daga cikin manyan shugabanni na duniya, yana karɓar miliyoyin daloli.

Asali: Twitter
Albashin shugaban kasar Amurka a shekara
Sai dai tashar BBC ta ce ba haka lamarin yake ba, domin shugabannin ƙasar Amurka ma’aikacin gwamnati ne, kuma albashinsa yana fitowa ne daga harajin da ‘yan ƙasa ke biya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A rahoton jaridar na 31 ga Oktobar 2024, wanda ta sabunta a ranar 21 ga Janairun 2025, ya nuna cewa tsohon shugaban Amurka, Joe Biden yana karɓar albashin $400,000 ne a shekara.
An ce, ko a lokacin da Donald Trump ya hau mulki a 2016, albashin shugaban ƙasar bai sauya ba, shi ne dai ake amfani da shi tun kafin ƙarni na 21.
Trump bai karbi albashi a mulkinsa na farko ba
A wa'adin mulkinsa na farko, Trump bai karɓi albashi ba, an ce yana raba shi ne ga ma'aikatun gwamnati daban-daban a kowace shekara.
A ƙarshen shekarar 2019, Trump ya ba da albashinsa ga ma’aikatar lafiya da walwala domin tallafa wa yaki da cutar COVID-19, kamar yadda wani kakakin Fadar White House ya sanar.
A cewar mujallar Forbes, Donald Trump wanda darajar dukiyarsa ta kai dala biliyan 5.1 a 2025, shi ne mafi arziki da ya taɓa zama shugaban ƙasar Amurka.
Yadda albashin shugaban Amurka yake
Rabe-raben albashi da alawus ɗin shugaban kasar Amurka:
- Albashi: $400,000 a shekara
- Alawus na bukatu: $50,000
- Nishaɗi: $19,000
- Gyaran Fadar White House: $100,000
- Kula da gida: Ya ƙunshi masu dafa abinci, masu shara da lambuna
- Lafiya da sufuri duka kyauta ne; shugaban na hawan jirgin Air Force One, jirgin sama na Marine One, da motar limosin.
- Ƙarin alawus: $100,000 na tafiye-tafiye a shekara, ba tare da biyan haraji ba
Sauyin albashi a tarihin Amurka
Tun daga 1789, lokacin da George Washington ya zama shugaban ƙasa na farko, sau biyar ne kacal aka sauya albashin shugaban ƙasa.
- 1789: $25,000 (kimanin $895,700 a yau)
- 1873: $50,000
- 1909: $75,000
- 1949: $100,000
- 1969: $200,000
- 2001: $400,000 (lokacin da majalisa ta ninka albashin)
Manufar biyan wannan albashin ita ce hana shugabanni cin hanci ko karkatar da dukiyar ƙasa.

Asali: UGC
Shugaban kasa ba shi ne mafi kololuwa ba
Idan albashi kaɗai za a kalla, shugaban ƙasa ba zai shiga cikin kashi 1% na Amurkawa masu kuɗi ba. Akwai ma'aikatan da ke samun albashin $788,000 a shekara.
Duk da haka, albashin shugaban ƙasa ya nunka matsakaicin albashin ɗan Amurka sau shida, wanda ke daukar $63,795 a shekara.
Bayan sauka daga mulki, an ce shugaban ƙasar Amurka zai ci gaba da samun fansho har ƙarshen rayuwarsa.
Rahoto ya nuna cewa ana biyan tsohon shugaban kasa kusan $244,000 a shekara tare da ba shi tsaro, kula da lafiyarsa da kuma biyan kudin tafiye-tafiye na aiki.
Albashin shugaban kasar Najeriya
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Shugaban hukumar RMAFC, Muhammed Shehu, ya bayyana cewa albashin shugabanni ba ya kai yadda mutane ke tunani da yawa.
A cewarsa, shugaban ƙasa na karɓar ƙasa da Naira miliyan 1.5 a kowane wata, yayin da wasu ma’aikatan CBN ke karɓar fiye da ministoci.
Rahotanni sun nuna cewa albashin ministoci da hadimai na da tsoka, kuma ana ganin ana iya amfani da su don gyara wasu sassa na gwamnati.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng