Gwamnatin Kano Ta Bankado Badakala a Tsarin Biyan Albashi, Ta Fadi Matakin Dauka
- Gwamnatin jihar Kano ta gano wani rashin gaskiya da ake aikatawa a wajen biyan albashin ma'aikatan ƙananan hukumomi
- Binciken da aka gudanar ya nuna cewa akwai ma'aikatan da suka yi ritaya ko suka mutu da ake ci gaba da biya albashi
- Gwamnatin ta bayyana cewa za ta ɗauki mataki kan duk wanda aka samu da hannu wajen aikata wannan aika-aika
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta bankado badaƙala a cikin tsarin biyan albashi na ma’aikatan ƙananan hukumomi.
Gwamnatin ta gano cewa aƙalla ma’aikata 247 sun mutu ko kuma sun yi ritaya, amma sun ci gaba da bayyana cikin waɗanda ke karɓar albashi.

Asali: Facebook
Wannan bayani yana ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai na ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano, Musa Muhammad, ya fitar, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin Kano ta gano ma'aikatan bogi
Binciken ya gano cewa sunayen ma’aikatan da suka mutu ko suka yi ritaya suna ci gaba da fitowa a cikin jerin waɗanda ake biya albashi, kuma ana ci gaba da tura musu albashi kamar yadda aka saba.
Adadin kuɗaɗen albashin da ake biyan wadannan ma’aikatan da suka mutu ko suka bar aiki ya kai N27,824,395.40 a cikin watan Maris na shekarar 2025 kaɗai.
“Gwamnatin jihar Kano tana ci gaba da ƙoƙarinta na gyara tsarin biyan albashi da tsaftace bayanan ma’aikata a faɗin jihar, inta samu gagarumar nasara wajen tsaftace tsarin."
"Sakamakon binciken tantance ma’aikata ya bayyana wata babbar matsala a tsarin biyan albashi na ƙananan hukumomi."
"An gano cewa mutane 247 ko dai sun yi ritaya ko sun mutu, amma har yanzu sunayensu na ci gaba da bayyana a tsarin biyan albashi, ana kuma biyan su albashi."
"Kuɗaɗen da aka biya ba bisa ƙa’ida ba sun kai Naira 27,824,395.40 a watan Maris 2025 kaɗai."
“Gwamnati ta gaggauta ɗaukar matakin mayar da kudaden da aka karɓa ba bisa ƙa’ida ba zuwa baitul malin ƙananan hukumomi, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike don gano waɗanda ke da hannu a wannan aiki."
- Musa Muhammad
Wane mataki gwamnatin za ta ɗauka?

Asali: Facebook
A cewar sanarwar, dawo da kudaden yana nuna jajircewar gwamnatin wajen tabbatar da gaskiya, riƙon amana da kuma tafiyar da dukiyar jama'a yadda ya dace.
“Gwamnati tana nan daram a kan ƙudirinta na kawar da duk wata barna a tsarin biyan albashi. Duk wanda aka samu da hannu a cikin wannan ɗanyen aiki za a bankaɗo shi, kuma za a ɗauki matakin doka a kansa."
- Musa Muhammad
Gwamna Abba ya biya ƴan fansho kudinsu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, ta biya bashin da ƴan fansho suka biyo.
Hukumar kula da fansho ta jihar ta bayyana cewa ta biya bashin N21bn daga cikin waɗanda ta gada daga wajen gwamnatocin baya.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa gwamnatin da ta gabata ta taɓa kuɗi a asusun ƴan fansho da sunan rance.
Asali: Legit.ng