Manyan Labarai A Yau
Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, ya zama abin magana kan rade-radin da ake yi na cewa zai koma jam'iyyar APC mai mulki.
Hukumar NCoS ta ce wani fursuna, Charles Okah ya cinna wa katifarsa wuta, wanda ya jawo hankalin jama'a, tana mai cewa babu fashewar bam ko hari daga waje.
Mai ba gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori shawara ta musamman kan harkokin kasuwanci da safara, Chief Love Shimite ya mutu, ƴan uwa suna zargin mijinta.
An samu tashin wata mummunar gobara wacce ta jawo asarar dukiya a birnin Kano. Gobarar ta lakume shaguna da ajujuwa da dama a unguwar Rijiyar Zaki.
Babban kusa a jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya, Segun Sowunmi, ya shawarci Peter Obi da ya dawo jam'iyyar kafin zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Hankula sun fara karkata kan batun babban zaben shekarar 2027. Alamu sun nuna cewa Shugaba Bola Tinubu na iya samun tikitin yin tazarce ba tare da hamayya ba.
Tsohon ministan tsaron Najeriya, Janar Theophilus Danjuma, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su tashi tsaye domin kare kansu saboda gwamnati ba za ta iya ba.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci a garin Kware da ke jihar Sokoto. 'Yan bindigan sun kona kasuwar garin tare da raunata mutane masu yawa.
Jami'an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun cafke wata hodar iblis da aka boye cikin littattafan addin don kai wa kasar Saudiyya.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari