'Yan Sanda Sun Kama 'Yar Chadi da ake Zargi da Kisan Kai a Kano
- Rundunar ’yan sandan Najeriya ta kama wata ’yar kasar Chadi, Mahadijiria Abdoulaye, da ake nema ruwa a jallo kan zargin kisan kai
- An kama Mahadijiria Abdoulaye ne a ranar 5 ga Agusta, 2026, a Railway Quarters da ke karamar hukumar Nasarawa a jihar Kano bayan bincike
- An mayar da wadda ake zargin zuwa N’Djamena domin fuskantar shari’a, yayin da ’yan sanda suka jaddada cewa ba a tabbatar da laifinta ba tukuna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar ’yan sandan Najeriya, ta hannun INTERPOL Nigeria, ta kama wata ’yar kasar Chadi, Mahadijiria Abdoulaye, wadda hukumomin kasar Chadi ke nema ruwa a jallo kan zargin hannu a wani shari’ar kisan kai.
An kama Abdoulaye a ranar 5 ga Agusta, 2026, a Railway Quarters da ke karamar hukumar Nasarawa a Jihar Kano, bayan musayar bayanan sirri.

Source: Getty Images
Nigerian Tribune ta kawo labarin cewa da kuma gudanar da samame na hadin gwiwa tsakanin hukumomin tsaron Najeriya da Chadi.
An kama yar Chadi a Kano
Jaridar Leadership ta kawo labarin cewa hukumomin Chadi, an azabtar da wata mata mai suna Nazik Mahamat Saleh har lahira a ranar 3 ga Mayu, 2026.
Bayan gudanar da bincike kan lamarin, Kotun Daukaka Kara ta N’Djamena ta bayar da sammacin kama Abdoulaye da wata da ake zargi mai suna Fatime Senoussi Mouktar a ranar 22 ga Yuni, 2026.
Rundunar ’yan sandan Najeriya ta ce bayan kama Abdoulaye, an mayar da ita zuwa N’Djamena, babban birnin Chadi, ta hanyar Lomé na kasar Togo, domin fuskantar matakan shari’a.
Za a yi bincike a Chadi
An gudanar da aikin ne tare da hadin gwiwar INTERPOL Nigeria da INTERPOL Chad, a wani bangare na hadin gwiwar kasashen biyu wajen gano tare da cafke mutanen da ake nema ruwa a jallo kan manyan laifuka.

Kara karanta wannan
Dalibai 4 na makarantar haddar Alkur'ani sun mutu lokaci guda a jihar Kano, an gano dalili

Source: Original
Rundunar ta ce lamarin ya sake nuna cewa masu laifi ba za su iya tsere wa hukunci kawai ta hanyar tsallaka iyakokin kasashe ba.
Sai dai hukumomin sun jaddada cewa Abdoulaye ba ta da laifi har sai wata kotu mai hurumin shari’a ta zauna, ta yi saurare sannan an tabbatar da laifinta da ikon doka.
An taya jami'an Chadi kama dan ta'adda
A baya, mun wallafa cewa hukumar tsaro ta Najeriya ta taimakawa kasar Chadi wurin tabbatar da kama wasu hatsabiban yan ta'adda da aka tabbatar suna addabar jama'a.
Sojojin Chadi sun kama ɗan marigayi Mohammed Yusuf, wanda shi ne ya kafa kungiyar Boko Haram a Najeriya wanda har yanzu ta ke kan gudanar da mugayen ayyukan daukar ran jama'a a sassa daban daban na Najeriya da Nijar.
An kama matashin mai shekaru 18 tare da wasu biyar da ake zargi suna da alaƙa da kungiyar yan ta'addan ISWAP a wani samame bayan an yi aikin hadin gwiwa tsakanin dakarun kasashen Najeriya da na Nijar.
Asali: Legit.ng
