'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Zamfara, an Hallaka Rayuka Masu Yawa

'Yan Bindiga Sun Kai Hare Hare a Zamfara, an Hallaka Rayuka Masu Yawa

  • An shiga jimami a jihar Zamfara bayan ƴan bindiga ɗauke da makamai sun hallaka aƙalla mutane 28 a wasu hare-hare
  • Miyagun ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a wasu ƙauyuka uku na ƙaramar hukumar Maru ta jihar
  • Dakarun sojoji sun kawo ɗauki a lokacin harin inda suka kashe da dama daga cikin tsagerun ƴan bindigan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Zamfara - Ƴan bindiga sun kashe aƙalla mutane 28, ciki har da masu haƙar ma’adanai 20 a jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun kai hare-haren ne a ranar Alhamis a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara
'Yan bindiga sun hallaka mutane 28 a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa hare-haren da suka auku da misalin ƙarfe 11:30 na safe, an kai su ne a ƙauyukan Gobirawa Chali, Damaga da Lugga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan bindiga sun yi ɓarna a Zamfara

Mazauna yankin sun bayyana harin a matsayin wanda ya zo ba zato ba tsammani kuma na mugunta, suka ce ƴan bindigan sun zo da yawa sosai.

A Gobirawa Chali, wanda shi ne ƙauyen da aka fi yin ɓarna, fiye da masu haƙar ma’adanai 20 ne suka rasa rayukansu bayan da ƴan bindigan ɗauke da makamai suka buɗewa wani wurin haƙar ma’adanai wuta.

Wani mazaunin yankin, Ismail Hassan, ya ce ƴan bindigan masu yawa sun buɗewa masu haƙar ma’adanai wuta a ranar Alhamis da rana, inda daga nan gobara ta kama, wanda hakan ya janyo asarar rayuka da dama.

Wani mazaunin yankin, Isah Ibrahim, ya tabbatar da cewa an gano gawarwaki 21 bayan harin, yayin da wasu da dama suka jikkata.

A ƙauyen Damaga kuma, rahotanni sun ce mutane biyar ne suka rasa rayukansu, yayin da a lokaci guda aka kashe mutane uku a Lugga.

Wani mazaunin Lugga ya bayyana yadda ƴan bindigan suka zagaye ƙauyen, suka riƙa harbi kan mai uwa da wabi sannan suka sace dabbobi.

“Sun kuma afka Damaga inda suka kashe mutane biyar. Ba mu san dalilin waɗannan hare-hare ba domin tun sama da shekara daya da ta gabata ba a kai mana hari ba."

- Wani mazaunin ƙauyen Lugga

Gwamna Dauda Lawal
'Yan bindiga sun kai hare-hare a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Dakarun sojoji sun kai ɗauki

Wata majiya daga yankin, wanda ta nemi a sakaya sunansa, ta ce adadin waɗanda suka mutu na iya ƙaruwa sosai da ba don saurin zuwan sojojin Najeriya ba.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojoji da kuma jirgin yaƙi sun iso lokacin harin, inda suka fafata da ƴan bindigan har suka kashe da dama daga cikinsu.

Da aka tuntuɓi, mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce bai samu cikakken bayani game da hare-haren ba.

Ƴan bindiga sun ƙaƙaba haraji a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan bindiga sun ɗauki matakin ƙaƙaɓa haraji ga wasu ƙauyuka 12 da ke jihar Zamfara.

Ƴan bindigan sun sanya harajin ne a ƙauyukan da ke ƙaramar hukumar Maru saboda zargin mutanen yankin da ba sojoji bayanai.

Sanyawa mutanen ƙauyukan harajin dai na zuwa ne bayan dakarun sojoji sun kai wani samame a maɓoyarsu da ke cikin daji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng