Manyan Labarai A Yau
'Yan ta'addan Boko Haram sun sake kulla wani sharri kan jami'an tsaro a jihar Ɓorno. Miyagun sun hallaka sojoji guda biyu bayan sun dasa bama-bamai a kan hanya.
Tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa ya bayyana cewa tsoon dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2023, Alhaji Atiku Abubakar zai fice daga jam'iyyar.
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya nuna damuwarsa kan rikicin Boko Haram. Gwamnan ya ce talauci da jahilci na taka rawa wajen ruruwar da rikicin ke yi.
Abdullahi Ganduje ya jagoranci kaddamar da masallacin Juma’a da ministar Abuja, Dr. Mariya ta gina a Bunkure, inda ya yabawa kokarinta wajen ci gaban addini.
Rikicin siyasa ya ɓarke tsakanin gwamnan jihar Neja, Bago da mataimakinsa Yakubu Garba, wanda aka ce ya fara kwashe kaya daga gidan gwamnati, da zummar barin aiki.
Bayan yada jita jitar cewa an kama Ahmad Isa mai Brekete Family, abokin aikin shi ya tabbatar da cewa ba kama shi aka yi ba. Ya ce Ordinary President ya tafi hutu ne
Hukumar kula da Alhazai ta Kwara ta ce za a fara jigilar farko ta alhazan a ranar 12 ga Mayu, yayin da ta ce an tanadi masauki da abinci har zuwa karshen Hajji.
Mataimakin gwamnan jihar Neja, Kwamared Yakubu Garba, ya fito ya yi magana kan rahotannin da ke cewa ya yi murabus daga mukaminsa. Ya ce ba gaskiya ba ne.
Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Salihu Lukman, ya caccaki gwamnatin Bola Ahmed Tinubu. Ya ce babu wani abin kirki da za ta tabuka.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari