Ranar Ma'aikata: Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Ranar Hutu
- Gwamnatin tarayyar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta ayyana sabuwar ranar hutu ga ma'aikata a faɗin ƙasar nan
- Ministan harkokin cikin gida a madadin gwamnatin tarayya ya ayyana ranar Alhamis, 1 ga watan Mayu a matsayin ranar hutu
- Olubunmi Tunji-Ojo ya ayyana ranar ne a matsayin lokacin hutu domin bikin ranar ma'aikata ta duniya wadda ake yi a kowace shekara
- Ministan ya yaba da jajircewa da sadaukarwar da ma'aikata suke nunawa wajen gudanar da ayyukan da suke yi a fadin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu ta ayyana ranar Alhamis a matsayin ranar hutu.
Gwamnatin tarayyar ta ba da hutun ne domin bikin ranar ma’aikata ta bana, wadda ake gudanarwa a kowace shekara a ranar, 1 ga watan Mayu.

Asali: Twitter
Ministan harkokin cikin, Olubunmi Tunji-Ojo, ya sanar da hakan a madadin gwamnatin tarayya, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya ta ba da hutu
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa a daren ranar Talata da babbar sakataren ma’aikatar harkokin cikin gida, Magdalene Ajani, ta sanyawa hannu, rahoton jaridar TheCable ya tabbatar.
Ministan ya jaddada buƙatar zaman lafiya domin haɓaka masana’antu da ci gaban tattalin arziki.
Olubunmi Tunji-Ojo ya yabawa ma’aikata bisa jajircewa da sadaukarwar da suke nunawa a wajen gudanar da ayyukansu.
Ya bayyana cewa ƙoƙarin ma’aikata ne ya fi taimakawa wajen gina ƙasa da kuma mutuncin da Najeriya ke da shi a cikin jerin ƙasashe na duniya.
Don haka ya buƙaci ma’aikata da su rungumi al’adar ƙirƙiro sababbin abubuwa da samar da ƙima a ayyukansu.
Ministan cikin gida ya yabawa ma'aikata

Asali: Facebook
"Akwai mutunci a cikin aiki, sadaukarwa da jajircewa wajen aikin da muke yi na da matukar muhimmanci wajen gina ƙasa.
"Ministan ya ƙarfafa gwiwar ma’aikata da su ɗaga matsayin aikinsu domin su taimaka wajen inganta shugabanci da tabbatar da cewa al’ummar Najeriya sun amfana da dukiyar ƙasa yadda ya kamata."
"Wannan gwamnati ta ƙudiri aniyar tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin kowane ɗan ƙasa da ƴan ƙasashen waje a cikin ƙasar nan."
"Yayin da ya yiwa ma’aikata fatan yin biki mai albarka, ministan ya buƙaci ƴan Najeriya da su ci gaba da kasancewa masu fata mai kyau, duba da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na da kishin cika alƙawurran da ke cikin shirin "sabon fata".
- Magdalene Ajani
Gwamnatin tarayya ta tantance jakadu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta shirya tura jakadu waɗanda za su wakilci ƙasar a ƙasashen duniya.
Gwamnatin ta kammala tantance mutanen da aka miƙa sunayensu domin zama jakadu a ofisoshin diflomasiyya na Najeriya da ke faɗin duniya.
Rahotanni sun bayyana cewa an kammala aikin tantancewa ta fannin binciken tsaro da tarihin kowane daga cikin mutanen da aka miƙa sunayensu.
Hakan na zuwa ne bayan Najeriya ta daɗe ba ta da jakadu a ƙasashen duniya tun bayan hawan Shugaba Tinubu kan mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng